yaa fahd nake so (4)

180 16 4
                                    

"mama! wae kin san ya fahd ashe baya son cat?" sha'hida takarashe maganar tana ture plate enta gefe.

gyada kai mama tayi "Allah ko?" sha'hida ta ce "eh, yanzu ma wurinsa zani ya cikan alkawari na"

"alkawarin me yayi miki?" anty zainobu ta tambayeta. "wasa zamuyi da teddie na amma bazan kai kitty ba, kar ya gudu" daria hameed ya danyi ya dau juice en shi ze sha.

fahd...ni ina na sanshi?

***
misalin karfe 4 na yamma

umni na zaune a parlour tana kallon window Alhaji Abubakar ya sauko daga stairs. dama ya riga ya san idan ta zauna ita kadai to fahd ta tuno.

kusa da ita ya koma ya zauna. a razane umni ta juyo da ta ganshi se tayi ajiyar zuciya ta sakar masa wani gajiyayen murmushi.

"mene yasaki tunani?" ya tambayeta ita kuma ta dena yaken da take ta mike tsaye.

shima tashi yayi ya rike hannun ta. "bana son ki damu kanki. ko me kike so idan kika fada zan miki" yar daria umni tayi ta kalle shi.

"ina ga... I'm pregnant"

kasa magana yayi ya fara kin ki na "d- da- dagaske??"

sunkuyar da kai umni tayi "eh ama ban tabbatar ba"

gyada kai Alhaji yayi ya rike hannun ta suka zauna. shuru ne ya dan biyo baya se kuma daga chan Alhaji ya daga hannu yayi salati ya godewa Allah.

"ki zauna gani nan zuwa" ya fada murya na rawa ya haura upstairs.

shuru umni tayi se kuma ta kasa zama ta mike tsaye. ko minti daya baya cika ba Alhaji ya sauko da hijabi a hannun sa da keys en motar sa.

cikin fara'a ya karasa inda take ya tsaya gaban ta. kasa tayi da idonta sabida tin asali bata saba da hada ido da shi ba har yanzu.

shi da kanshi ya zura mata hijab en ya rike hannun ta sukayi hanyar waje.

***
Dama akwai wata me aiki da hajiya halima take biya kudi tana bata labarin kome ke faruwa a gidan da umni take zaune. sunan yar aikin ta atika, atika yarinya ce da bata fi shekaru sha daya sha biyu  ba. baka ce ita me karamin hanci gajera kuma siriria.

Atika na ganin su umni sun fito suna ta farin ciki se ta karasa da sauri ta tsuguna gabansu. "ina wuni"

a mutunce umni ta amsa sallamar tare da tambayar ta ya lafiyar ta shi kuma alhaji yayi gaba sabida ya kunna motar.

"lafiya kalau. hajiya, ficewa zaki?" atika ta tambaye ta tana kafta ido. "eh atika, kiyi min addua"

atika zata kara magana zainura ta zo itama ta gaida umni ta ja atika sukayi gaba.

"wallahi atika ki dena abin da kike yi. kamar wata mara ilimi? meye hajiya bata yi mana? abincin da kike ci anan ita hajiya babba ta taba barin kinji ko kanshin sa ne?"

ture zainura atika tayi ta wuce. zainura tayi ajiyar zuciya ta bita a baya

Salam alaikum. na gode da damuwar da kuka nuna akai na. wata yar matsala aka samu ama insha'allah zaku na jina yanzu.

pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now