rayuwar mu (3)

480 46 1
                                    

Da aka gama paper, fahd ne karshen fitowa daka aji dan ko second ashirin ba'ayi ba da fitowar shi aka kuma komawa.

Nan ma se wurin daya da rabi teacher ta karbi paper sannan ya fito. Sauran mutane kadan a makarantar. Basufi su shida ba.

Shima hanyar gida yayi, yana tafiya kansa a kasa kamar kullum har taje gida.

Daya koma, wace rana? Ya tarar da wuta a gida. Kodai ba komai zega haske. Karar watsa ruwa ne ya tabbatar masa da umni tana wanka.

Kofar gidansu aka kwankwasa ya  karasa ya bude. Umni ya gani tasa blue abaya.

Tana ganin shi jikin jikinta yadda yake kama da yar uwarta ta rungume sa tana kuka.

Shi dai yasan umni nada tawada a gefen fuskarta ama gashi wannan ita babu? Kuma ko kalan turaren ba iri daya bane.

Kwace kansa daka gareta yayi ya koma yana kokarin turo kofar ta yi hanzarin rike hannunshi.

Ta sakar masa murmushin da har hakorin makanta ya bayana "Baby boy hear me out mna"

Fahd dake faman kwace kanshi ina ze ji wani turanci? Cigaba yayi da kokarin guduwa.

Umni ce ta fito sanye cikun hijabi gannin me ke faruwa tayi saurin janye fahd a firgice. Matar ta bita da ido, se alokacin umni taga fuskarta.

"Zarah?"

Wadda aka kira zara ta fashe da kuka ta rungume umni. "Nafisat meyasa kika bar rayuwar mu? Why did you punish us for somthing we didn't do? Why?"

Nagode.

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now