kadara ce (3)

615 47 8
                                    

ranar da aka gama rubuta exams zia taje ajin su fahd da kanta ta tambayi teacher en yace mata ae an cire fahd daga makarantar.

address ta tambaya yace shima be sani ba.

ajiyar zuciya tayi tace "lallai ma friend" bata kara tambayar sa komai ba ta fice a ajin.

tana tafiya tana tunani. wata kila yazo endai an tashi

aiko har aka tashi ba fahd babu alamar sa. hakura tayi ta bi driver suka tafi gida.

tana zuwa gida ta fada wanka.

koda ta fito shiryawa tayi cikin kaya riga yellow da jeans wando.

parlour ta koma ta zauna ta kurawa tv ido.

gashi an kisa birthday enta nan da kwana uku. abbanta yace daman anayin birthday za ta tafi karatu.

ko ina zan kara haduwa da friend oho. ta fada cikin ranta.

a chan bangaren hajiya sa'adatu kullum umni seta yo mata waya ta hada ta da fahd seta ce wae baya nan ko kuma ya yi barci.

a zahiri kuwa tin ranar da a ka kai umni gidan ta hajiya sa'a bata kara sa fahd a idon ta ba. ba ruwan ta da ko me yake ciki

ganin bata iya samun fahd ta hanyar hajiya sa'a umni ta gwada kiran minoo

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now