mijin tsohuwa (1)

701 45 0
                                    

Anyi sati biyu da haka, ranar asabar ummi ta gama shirinta tsaf na tafiya gidan grammy. Ta juya fahd da yake zaune a kofar daki ya rafka uban ta gumi yana kallon ta.

"Fahd taso mutafi" yaji ta furta kamar a mafarki "umni dagaske?" Gyada kai tayi tana murmushi tace "ko bakason zuwa?" Ai tini yayi zumbur ya mike ya nufi daki ya goyo jakar makarantar shi. Daman ya rigada yayi wanka ya shirya.

Uhmm kawai umni tace ta rufe gida suka fita. Napep ne yakai su har kofar gidan umni ta dauko kudi ta basa ama tik yaki wai shi 350 zaya karba ita kuma umni ta ki sabida 120 sukayi dashi

Me napep ya kafe shi 350 za a bashi. Shiko gannin irin kammanin su da girman gidan da zasu shiga yasa sa kafewa. Umni dai kwata kwata 500 ce a hannun ta kuma idan ya karbe thom ya cuce su.

Suna tsaye wata gray mota tayi parking da gefen wurin. A hankali aka bude kofar ya zuro kafar shi ta dama kamin jikin shi ya fito waje.

Mutumin me kimanin shekaru 43 dogo ne chocolate color yana sanye cikin babbar riga da gani daurin aure ya nufa.  Cikin takunshi irin na manya ya iski inda suke yayi salama

"Meke faruwa ne haka?" Ya tambayi me napep, nan me napep ya kwashe komi ya fadi masa ita umni batayi magana ba ta kara rike hannun fahd daya kurawa motar mutumin ido.

Me napep na gani mutumin ya zaro dubu daya ya bashi ya kuma gaya masa ya bar chanjin. Umni sankuyar da kan ta tayi ta ce "nagode alhaji"

"Ba komi, sunana abuBakar"

Bata ce komi ba ta gyada kai ta ja hannun fahd suka shige cikin gidan.

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now