tori (3)

525 40 2
                                    

Su zia basu dawo daga gidan auntyn su ba se wurin goma na dare. Tana shiga dakinta ta hau rage kayan jikinta sannan ta fada wonka.

Koda ta fito cikin silk riga da wondon barci tayi ta hau gado. Dayake daman tayi sallah a chan gidan auntyn nata ne yasa kawai ta kunna tablet enta (wayarta ta fashe) ta hau instagram.

Gani tayi ansa Za0fficial_hamid started following you. Tabe baki tayi, dan ta saba yi da yan rainin hankali.

Profile enshi ta bude, nan taga bio ya rubuta 'daddy's prince, momma's boi' hotuna ta fara dubawa nan kuwa tasha kallo dan gayen ya gama haduwa ajin karshe. Shi irin hasken hutu ne dashi na black Americans, ha hanci ba karya.

Daga irin kayan dayake sawa har motar dayake hawa ba na wasa bane.

Wani hotonshi da yayi shi da mom da dad enshi a grad en shi ta shiga.

Anan tagane mamanshi ce baka yayinda babanshi ke fari kaman ka sa hannu jini ya fito.

Fuskar babanshi tayi enlarging.  Ita dai tana ta bazarin a enda ta san wannan fuska.

Hade gira tayi ta fita daka cikin instagram en gaba daya ta kwanta.

Koma waye kai baka dame ni ba!

Nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now