kadara ce (2)

494 38 6
                                    

shuru yayi ganin a enda yake. duk da a zuciyar sa se addu'a yake ace mafarki yake cikin mafarki amma yasan ba hakan bane.

mikewa yayi daga kan gadon ya shiga en suit yayi brush. yana cikin dauraye face ensa yaji anyi wata guda (buda?)

tunani ya farayi... auren wa ake yi? fita yayi daga cikin bandakin ya bude kofar dakin sa ya leka... gani yayi nanny da busboys auna ta zurga zurga.

wadda ta nuna masa dakin shi giya ya gano a cikin turmu tsutsun tana wa wani magana. be bata lokaci ba ya nufi wurin ta duk da kuwa har yanzu kayan barci ne a jikin sa irin riga da wando (pjs) light blue.

seda ya je daf da bayan ta se kuma ya tuno .... banfa san sunan ta ba.

mocking smile ya sakar wa kansa a zuciyar sa ya ce da kansa soko kawai.

juyo wa tayi ta kusa karo da shi. "ah... fahd? me ya faru?" ta tambaye sa tana mamaki.

(na tuno fa ban muku kwatancen kamar ita nannyn ba ko😅)

Ita dai sunan ta minoo, shekarar ta goma sha takwas. baka ce ita me dara daran idanu dakuma karamin hanci da dan madaidai cin baki. siririya ce kuma doguwa.

tana da training sosai sabida wadda ta kawo ta daga kano ta ladabtar da su sosai shiyasa haj sa'adatu take son aikin ta duk da kuwa tana sa a tafke ta idan taga dama.

kullum a natse take abu da wuya kamin tayi laifi hakan ya karbo mata mukamin zama head of hygiene ta gidan. aikin ta ne ta kulla da tsaftar komai tindaga sama har kasa a gidan.

cigaba

"naji... ana guda?" ya tambaye ta a hankali. tausayi ya bata ta rike hannun sa. "zo muje zan gaya maka komai.

a zuciyar tana jin ba dadin abun da hajiyar tayi. a jiya ta bada umarni a zuba masa abin barci a ruwa. duk da minoo ta sayo mafi rashin sauri da karfin aiki hakan be hana mugun nifin da hajiyar ta kulla ba.

seda ya gama shiryawa tace ya fara cin abinci. "umni" fahd ya tambaye ta. shurun da ta danyi yasa shi gane akwai wani abu.

rasa yadda zata shawo kanshi minoo tayi shikuma ya zuba mata ido. ajiyar zuciya tayi.

"fahd..." sekuma sauran abin da zata ce ya tsaya mata a wuyan ta data ga yana yi mata smile har dimple ensa ya lotsa.

"auren... umni na akeyi ko?" ya kuma tambayanta duk da yasan amsar. daga kai kawai tayi.

a take smile ensa ya gushe. "dama banyi sallah ba" kawai ya ce sa'annan ya fada bandaki.

ajiyar zuciya minoo tayi tana tuno da abin da umni ta fada mata kamin a kai ta... seda ta same ta ita kadai ta roketa ta kulla da shi. abin ya bawad minoo tausayi kuma tayi mata alkawarin hakan.

tashi tayi ta fita ta turo kofar dan tasan yana bukatar kadaici a lokacin.

shidai fahd yana tura kofar bandakin ya zauna ya hada kai da gwiwa yana ta kuka. shike nan an rabashi da umnin shi ba dan ta mutu ba.

nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now