tuhuma (2)

616 41 0
                                    

Ta shagala da kallon titi ta ji 'kkkkkkrrrrr" yaja wani birki, kanta ne ya bugu a jikin window wurin ya fashe.

Dishi dishi da fara gani kamin tayi passinh out, bata bude idonta ba se bayan 2 minutes ama ji tayi kaman tayi awanni. Wani azaba ne ya ratsa kanta tayi saurin sa hannu se taji wani abu me dumi ta ware ido. Me zata gani? Jini jawur yayi darr a tafin hannunta.

A furgit ta waiga gefen da ya jabir yake ta ganshi ya dafe kirginshi yana ta haki kaman wanda yayi gudu. Cire seat belt inta tayi ta hau kokarin dawo dashi cikin hankalin shi amma to no avail. Tunowa tayi da wayanta tayi saurin dailing number in mommy.

Tana kira mommy ta daga, jiki na rawa zia ta fara magana cikin kuka "mommy...ya jabir....ya jabir bashi da lafiya...mommy"

Hankalin mommy ya ta tashi "kuna ina? yanzu zan turo a dauke ku"

Fahd da grammy na zaune a parlour kaman kullum yana nuna mata note books inshi. Abin mamaki shine ba fail ko daya tin da yafara nuna mata, sede handwriting inshi akwai sauran yarinta a ciki.

Waya aka bugo mata, hakan yasa ta kalli fahd "mikon wayar kaji mijina" gyada kai yayi ya tashi ya dauko mata wayan ta amsa

"Subhanallah" ta furta tana mike wa ta nufi daki "fahd kira umni muje ku rakani asibiti" umni ce ta juyo salati tayi hanzarin karasawa cikin parlour tana tambaysn fahd me ya faru.

"Asibiti" ya fada yana nuna daki "bata da lafiya ne?" Girgiza mata kai yayi alaman a a. Umni ta dafe kanta, idan yan kan fahd suka dawo abinsa se allah.

Grammy ce ta fito tana ta trying number in driver ama taki shiga "wannan mutumin! Yanzu ku taso mu hau mota" umni ce ta mike ta rike hannun grammy "karki damu muje zan iya jan motar" kallin tuhumar da grammy tayi mata ne yasata saurin cewa

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now