marayan dole (1)

311 37 4
                                    

Da Alhaji AbuBakar ya kula kwata kwata hankalinta baya kansa se ya tura kofar ya rufe a hankali sa'annan ya soma cire shoes ensa.

kara wayar ta tayi shi ne ya dan dago kai ita kuma a lokacin ta mike zumbur ta amsa wayar

"Fahd... lafiya kalau.... kana cin abinci kuwa? ok minoo tana baka... thom... uhmm kana jina ko? bana so ka na fita yawo... au daria kake ko?"

tin da ta fara wayar AbuBakar yake kallon yadda take ta washe baki tana goge kwala hakan ya sanar da shi wata killa da yaron nata take waya.

har ya raba ya zagaye ta ya haye bene bata kula dashi ba.

a chan daya bangaren kuma fahd na zaune da aka bashi dan a cewar sa shi ba dakinsa bane, duk fitilun akashe suke ba wanj haske da ke ratsa labulan. iya screen en wayar minoo kadai wani source en light a dakin.

fahd rabe a kan gado yana ta kallon screen en kamar umni zata fito daga ciki sedai kuma hakan ba ne faruwa ne ba.

sautin muryar umni kawai yake ji alamar ita murna take sosai shiyasa idan ta fadi wani abin kawai yake dariya ba dan wai yana jinta ba

A zahiri ma ji yake kamar ya hadiyi zuciya ya mutu sabida an rabashi da ita an maida shi marayan dole. "fahd kana ji na?" cewar umni

"uhm" kawai ya furta tare da ajiye wayar a kan pillow

shiru tayi tace "nasan halinka fa? kana da zurfin ciki, duk abinda yake damun ka kar ka boyen shi. promise?"

be amsa ba ya hada kai da gwiwa.

kiran sunan shi ta koma yi ama shiru. screen en wayar ta umni ta kuma dubawa nan ta ga wae ashe call en ya kare.

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now