tori (2)

520 39 2
                                    

Saurin goge kwalar dake umni idonta tayi kamin grammy ta ankara.

"Umni. Grammy tace mu tafi da tori gida" fahd ya karaso yana mata nuni da kofar da aka shigar da akkun.

"Tori? Kana nufin akku" umni ta sunkuyo ta sa hannayen ta fan ja kumatun fahd. "Ae kai ne tori"

Daria grammy tayi irin ta manyan nan ta gyara glasses enta  "wae tori yana nufin tsuntsu a harshen Japanese"

"Aaaa. Gaskiya ne" umni ta fada cikin daria. Ana cikin haka ne wannan poster en dake jakar umni ta fado cikin rashin sani umni ta mike tare da fadin "na tafi na duba ko an gama?".

"Thom. Daman ni ina nan nida miji na" grammy ta janyo fahd jikin ta. Smile umni tayi ta juya ta tafi.

Har sun juya grammy ta kula da poster en ta tsugunna a dauka. Dayakea dunkule take fahd shima be gane ta ba. "Bari kaga na duba sunna. Idan me amfani ce mu baiwa receptionist"

Gyada kai had yayi kawai sa'annan ya baida hankalinsa wani wurin. Grammy na warware takardar tayi karo da hoton umni.

Bi tayi ta karanta rubutun dake jiki kamar haka.

Missing person issue.
Any information related to this person is wanted with extreme importance.
N

AFISAHT AHMED YUSUF HAKIM

Sekuma enda aka rubuta adadin kudin da adress da number en waya.

Shuru grammy tayi tana mamakin abinda ta karanta.  Wato nafisat jika take da yusuf hakim?

"Sun fito" umni ta fada tana gyara zaman jakarta dake hange a kafadar ta. "Grammy?"

Daga kai grammy tayi haryanzu rabin hankalinta na cikin nazari.

"Zamu office ne muyi signing"

Nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now