mijin tsohuwa (2)

654 46 0
                                    

Da salamarsu suka shiga me gadi ya nuna masu hanyar cikin gidan. Grammy na zaune tana karasa kallon wani series da ake yi na the mentalist taji salamar umni.

Da murmushi ta amsa suka shiga palon suka gaishe da ita. Da fara'arta ta tarbe su. Ta kawo masu lemon anibi da kankana. Shidai fahd wasanshi yake tayi da hannun sa.

Umni tace zata tashi ta fara aikin, har fahd ya tashi grammy tayi kiranshi ya zauna kusa da ita.

Kallon umni yayi ta gyada mashi kai, ya je ya zauna gefen grammy ita ko umni ta wuce.

Abinka da me son yara ba ajima ba suka saba. Yayi tabaiwa grammy labari kalla kalla itama ta biye masa.

Suna cikin haka umni ta dawo "hajiya me za'a dafa?" Grammy dan bata fuska tayi "i told you kina kira na grammy kuma ba sekin dafa komi ba, ae aikin da kika sha ya isa"

"A a wallah, ba komi dama na gama da wuri kuma munyi dake se biyar zamna tafiya" shiru grammy tayi ta kalla fahd " me kake gani ayi? eye mijin tsohuwa?"

Shashen Alhaji abubakar

Yana sa kafar shi a cikin gidan ba abin da ya fara ji se muryar matar shi hajiya halima da kukan yar aikin su najah.

"Hajiya don allah don annabi kiyi hakuri! Kuskure na ne"

"Ae yau me rabani da ke seya shirya! Ni zaki cuta?"

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now