tori (1)

531 39 2
                                    

Alhaji Abubarkar ne ya sakko daga bisa motar ya karasa bakin gate yayi masu gadi salama.

"Dan allah ina neman me gidan nan?" Ya tambaya. "Me gidan nan baya kasar a yanzu" gyada kai alhaji Abubarkar yayi ya juya ze tafi se ga umni ta karaso. Seda ta gaida su ta shige ciki.

Binta alhaji Abubarkar yayi da kallo. Se da wayar shi ta hau ruri ya dawo hankalinshi. Ganin me kiransa ne yasa ranshi ya baci. Ita bata taba kira se idan tana bukatar wani abu.

Be daga ba ya daga musu hannu alamar salama sannan juya ta shige motar.

Umni na shiga ta tarar grammy da fahd a garden sun durkusa suna kallon wani abu. Data karasa ne taga wata yar karamar akku red colour a hannun.  "Subhanallah mene ya same ta?" Umni ta tambaya. "Umni ta fado. Muna zaune ne" fahd fada yana mikewa tsaye.

"Yauwa yata. Daman wurin veterinary hospital zaki kaimu" cewar grammy. "Thom" umni ta ce ta shiga parlour ta daukowa grammy hijab da keys en motar.

Basu wani tarar da layi ba dayake ba a wani dau rayuwar dabbobi da matsala ba. Wani mutum ne ya karbi akkun ya shigar da ita wani daki. Ita kuma grammy ta kamo hannun fahd suka tafi kantin dake hade da asibitin suka sayo keji me kyau da kuma abinci kala kala. Har kwanika seda grammy tasa aka zabo ma akku.

Har lokacin dasu ka dawo ba'a fito da akku ba. Umni ita dai se kallonsu take.  A ranta ta ce

Daman kakar ka zata nuna maka irin wannan kaunar.

Nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now