kaskanci (4)

764 61 2
                                    

A dari zia ta shiga gidan su gram ta rungume kakarta "grammy nayi kewa naki sosai!" Grammy rungume zia tayi itama "sannu da zuwa aziza ya karatu?" Turo baki zia tayi sabida batasan dalilin da gram gram take son kiranta da wannan sunan.

Mommy ce ta shigo da salama ta zubawa zia ido "Thom seki je ki dauko kaya naki silly girl" zia rufe baki tayi "wallah na manta" ta karbi key in ta wuce.

Dawowarta ta tarar da mommynta har su yi salama zata fito. Kiss ta manna mawa mommy a kunci " da magrib zan aiko jabir ya dauke ki" mommy ta ce "okie aje lafiya"

"Amin zia" nan mommy ta hau mota ta bata gas

"aziza naga kina fama da leda? Lafiya dai ko?" Grammy ta tambaye ts cikin tsokana. "All is well wallah kawai kayan karatu ne"

"Allah ya sa albarka"

"Amin grammy"

Suna cikin hira me aikin grammy tazo "salama alekum!" Rufe kunne zia tayi tana yamutse fuska bata taba jin salama mara dadi irin wannan ba, kaman wani sakon mutuwa?.

Amsawa grammy tayi me aikin ta karaso daga ciki "ya gajiya?" Ta gaida grammy.
" lafiya kalau" tashi tayi ta wuce compound inda take shara.

Kallo kallo grammy da zia sukayi. "Grammy bara na shiga kitchen I'm thristy" zia ta fada tana mikewa tsaye

Kofar kitchen zia ta ga matar na shirya sharewa tayi saurin isa wurin"sannu" ta fada da zata wuce ita matar kuwa matar ta faro yabonta seda zia taji ta tsani kanta

Saurin komawa parlor tayi ta samu wuri ta zauna a kusa da grammy suka cigaba da hirar su hankalin kowa a kwance.

Ana haka har sun fara kallon korean film me aikin ta kuma rafka salama. "Haba hansai? Kamar gidan kurma?"

"Umm hajiya daman maganan nan da nace zan maki ne" hansai tayi maganar hade da sassauta muryarta "ina jinki?" Grammy ta amsa hankalinta be bar kan tv in ba.

"Akwai wani gida a inda nake. Matar gidan da ciki tazo ta haifu shekaru sufi goma kenan, kuma agaskiya kowa na anguwar mu sheda ne na dan nata yana son ya zame mana fitina." Daka tawa tayi ta fashe da wani matsanancin kuka "Ya fara harka da mata kuma duk karancin shekarun shi baya fita ko islamiya idan ma yafito da sabon ciwo a jikinshi zaka ganshi, wallahi abin tausayi yake bani." Shesekar kuka take kaman nufashinta zaya dauke ta kuma cewa " ko magana beya yi yaron, gashi da sata kaman wani babba.. Matar tanason ta bar danta ya watse gashi ya rame abin dai wallahi bakyau kuma har yanzu ba alamar yan uwanta zasu neme ta"

Ba iya grammy ba har zia seda ta ji tausayin hansai ama ita grammy bata yanke hukunci seda hujja. "Ina son naga wannan matar na tambayeta da kaina idan bayaninta be gamsar dani ba se hukuma ta kula da lafiyar yara ta amshi dan akaisa gidan marayu"

Kada kai hansai tayi tana goge kwallar idonta. Kallo grammy ta karayi mawa hansai ta dan tattabo zia "dauko paper ki kwafar mini adress na gidan. Dakaina zana shirya gobe naje"

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now