rayuwar mu (1)

533 41 4
                                    

"Na tafi class" ta mike har zata fita se kuma ta dawo ta hargatsa ma fahd gashi sa'anan ta juya ta fice.

Shidai fahd yadda ta barshi yake kaman mutum mutumi. Seda tayi mintina da tafiya shima ya tashi ya fice yana shafa kuncin shi.

A chan bangaren Alhaji Abubakar kuma tin da duhu duhu shirya ya tafi gidan yayar shi da ke ta faman neman shi.

Hour 6 drive yayi, be isa gusau ba se wurin sha daya na safe. Daman tini an riga an san da zuwanshi.

Yana zuwa yayar shi da yayanta suka tarbe shi sosai. Dayake mijin ta baya kasar ne basu samu sun hadu ba ama sunyi waya sun gaisa.

"Ko zaka shiga daki ka huta ne?"
Hajiya zainab ta tambaye shi bayan sun gaisa. "Ehn. Ina son fama indan watsa ruwa" ya gyada kai yana mikewa.

Itama tashi tayi daka kan kujerar da take a kai ta zaman mutum biyu "tor idan ka kintsa inaso muyi wata magana"

"Ba matsala" kawai yace ama shi kanshi yasan da matsala babba ma kuwa tinda ta neme shi cikun gaggawa haka.

Seda aka sauko daka sallar duhr suka samu suka zauna. Yaranta na islamiya so zasu yi magana batare da wani jinkiri ba.

"Lantana?? Kawo mana tea mna?" Hajiya zainab ta sanar da mae aikinta sannan ta samu wuri ta zauna a kujera me facing enshi.

"Abubakar.  Abinda yasa na kiraka daman. Inaso muyi magana akan auren ka"

Nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now