tuhuma (4)

628 55 2
                                    

"Ok fahd. Ka gaji ko? Zo nan ka kwanta"

Kallon umni yayi ita kuma tayi murumushi, dukda hankalinta be kwanta ba. Allah dai yasa ba ciwon hauka ne da shiba.

Mikewa yayi ya je enda mommy ta ke zaune. Nanta mike ta ce "hau nan ka kwanta" thom ya amsa kawai ya cire takalminshi ya haye samman gado. Ba dadewa barci ya dauke shi.

Daman giya ba wuta ga zafi hakan yasa beyi wanni barcin arziki ba. Hira mommy ta fara jan umni har ta saki jiki suka gaisa. Se a sannan wae mommy tasan wai fahd dan cikin tane.

Zia bata bisu asibiti ba. Daddy yasa aka kaita gida family doctor yayimata first aid ta samu wuri ta kwanta.

Karfe 6 ta farka tayi saurin rama salolinta sanan ta sauka  a lokacin su mommy sun dawo har daddy na shirin komawa dan baze yiwu ace an bar mara lafiya shi dayaba

"Daddy ka wuce?" zia ta tambayi daddy tana karasa saukowa. "Eh ya jikin?"

"Lafiya. Daddy kaci abinci kuwa

Murmushi daddy tayi tare da dan gayra hulanshi "naci mana. Yanzu ma ban dadeba"

Mommy ce ta fito daga kitchen ta mikawa daddy basket "ga kayan breakfast ko da ya tashi da wuri"

Once a week update from today

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now