Damfara (3)

278 24 5
                                    

tin abinda ya faru so biyu abubakar ya leko ya duba su umni. dama dai girkin su juyin sati sati suke itada halima. ba yadda hajjo batayi ba umni ta dawo da fahd gidaa umni ta ki.

yanzu ma haka waya suke inda hajjo take cewa "kinga nafisat. kiyi wa kanki fada, nasan abinda ya faru misunderstanding ne kawai. kila ma a makaranta ya je ya tabo shi chemical en yaci"

"eh na sani" nafisat tace a takaice. shuru hajjo tayi tace mata "ina son fahd kamar na hadiye shi nafisat. banaso naga baya kusa dani. kuma tsohon ku yana ta bibiyar shi. ga makaranta. ga kuma kar ya takura ku anan"

ajiyar zuciya umni tayi "hajiya yanzu ina da dan wani abu dana keyi zan kira ki"

a haka sukayi sallama.

fahd na zaune yana kallonta har ta gama wayar ta dawo kusa dashi ta zauna. "umni... nima inaga"

toshe masa baki tayi da donut en dake hannunta tace "fahd idan ana cin abinci ba'a magana"

daga nan yayi shuru da maganar tafiyar sa.

ita kuma umni a zuciyar ta tace

ae duk wanda yace fahd ya takura masa bansan me zanyi dashi ba

"umni ina so na koma makaranta" ya fada da sauri.

kallonshi ta danyi tayi murmushi. "ae uniform enka na nan. se nasaka a kaika ko gobe ma"

***
"daddy, mommy. na wuce gidan Grammy" zia ta karashe maganar tana hugging ensu. ya jabir yace "kiyi sauri mu wuce"

seda tayi gama yayi sallama da su daddy y biyo ta a baya.

"kina ta iyayi aure zamuyi miki mu huta" ya fada lokacin da ya fita daga harabar.

daria zia tayi. "haba yayana ni na isa na riga yayata shiga" murmushi ya jabir yayi har hakoransa suka baiyana.

"shiyasa nake ji dake wallahi sis kin iya hure kunne"

haka sukayi ta hira har suka isa gidan grammy.

PP-PANDA

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now