binkice (1)

712 49 0
                                    

Washe gari, umni na shirin fita sarar da turarukan konawa kamar yadda ta saba idan fahd ya wuce makarantar boko taji ana kwankwasa kofar gida.

Goge hannunta a wani dan duster tayi ta mike tsaye tare da hanzarin bude kofar gida.

Wata dattijuwa ta gani fara wadda zata iya yin shekaru 70 a duniya. Sanye take cikin ash colour in abaya, ta sa hijab dogo me hannu.

"Ina wuni," umni a fada tare da dan rutsunawa, amsawa datijuwar tayi da murmushi "ki shigo mna..."

Waje umni ta shimfida mata wata karamar tabarma ta zauna. Umni ta kowa abinci da ruwa ta sami waje ta tshuguna ta shukuyar da kanta.

"Baki gane niba ko? Ni sunana hajiya amina yakubu ladan. Nazo ne nayi wani dan binkice akan ki"

Gaban umni yayi muguwar faduwa da hajiya amina tayi maganar binkice hakan yasa ta fadi. "Ban gane ba?"

"Wato korafi aka kawo mani gami da danki. Shi ya yake da suna?"

"Muhammad ama ana kiranshi fahd. Wane irin korafi?"

Nan hajiya amina ta kwashe komi ta gaya Mata ama bata fadi mata ko wacece ta kowa ma ita hajiya aminan zanchen ba.

"Hajiya wallah sharri aka man. Banni taba zinna ba. Kuma abinda yasa fahd baya fita waje gudun tsangwama da bakin mutane yasa a gida yayi saukarshi. Maganan sata beya fita balantana ace ga abin da ya dauka kuma ni sheda ce akan hakan. Karatu ne yake kaisa makaranta ba komi ba, da an tashi thom ya dauko hanyar gida"

Shiru ne ya biyo baya kamin hajiya amina tace "duk wannan zan sheda idan shi fahd in ya dawo. Ko akwai inda zaki ne?"

Girgiza kai tayi "a a ina gida"

Sauke ajiyar zuciya hajiya amina tayi "daga ina kike?"

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now