kaskanci (1)

952 71 2
                                    

Kasancewar yau litinin yasa hanyar anguwar su fahd take a cike dam da mutane kamar koda yaushe kanshi a kasa yake tafiya dalilin hakan kuwa shine umnin shi tana fargaban bakin mutane.

Wata kwana ya yanka wadda babir ma da kyar ze iyabi. Kayin cike yake da gidajen ma talauta wasu ma katangar ta fada. Tin a bakin layin aka fara rakashi da kallo me cike da tsamtsami.

Wani karamin gida ya shiga daki biyu ne daya suna kwana dayan kuma ya zama kitchen ba palour se bandaki da  tsakar gida. Gidan dai kwata-kwata baya ci ace an kirasa gidaba. Amma duk da haka tsaf tsaf yake. Babu datti ko kadan a kan sumintin an wanke shi kal and share an kunna turaran wuta.

Mahaifiyar sa ya tarar a zaune a kofar dakin tana tsince shinkafar hausa yayi saurin karasowa tare da salama. "Ummnni na dawo" dagowa tayi fuskar ta dauke da murmushi ta ajiye kwanon gife guda "sannu da zuwa fahd, zo nan let me hug you" umni ta fada da sauti cike da kauna.

Gaban ta ya ja kafarsa ya zauna ita kuma ta rungume sa tana shafa tattausar sumarshi. "Yau ka dade mene ya sami face naka?" Ta tambaye sa yayin da ta kula akwai bandage a kuncinsa hade da dan girgiza kafadun shi.

"Umm friend na tsaya kuma kofa ce ta buge ni." Yayi karya yana smiling har dimple insa suka lotsa kaman gaske. Hankalin umni ya dan kwanta "na dora maka ruwa yanzu abin da nakeso shine ka wuce kai sallah kaiyi wanka se kaci abinci"

Gyada kai fahd yayi sannan ya mike ya nufi daki. Haka yayi sallah ya shirya cikin rigarshi orange da brown shorts insa. Ya je ya dauko abincin sa yaja ya zauna.

"Umni guess what?" Ya tambaye ta. Umni ta gama gyaran ta juyo kansa "what?"
Tashi taga yayi ya dauko jakan shi ta makaranta me hoton spiderman ya bude zip nan ya zaro oreos cookie da cway unopened and intact.

"Fahd ina ka samosu wannan?"

"Friend gave them to me" ya amsa tare da maida hankalin shi kan abinci, dama tin hasali Allahn daya yi sa baya dora mashi kwadayi ba

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now