Dafara (1)

169 15 1
                                    

hajjo ce ta fara kiran wayar umni bata dauka har awa daya ta saki ajiyar zuciya.

"motswweee ya akayi hakan ta faru?" ta fada tana zagaye a dakinta

duk abinda zaya faru bazan bari a raba dukiyar nan ba. dukiyar nafisat ta na boye a karkashen hanci na. 

tayi hucci tana danna hancin ta da karfi.

dole se fahd ya zama a hannu na... dole ne

wata zuciyar tace mata

kina da tabbas zaki rayu har kici gadon ita nafisatun?

wuri ta samu ta zauna tana nazari akan matakin da zata dauka akan hakan.

***
Motar Alhaji abubakar na parking masu aiki suka zo tarar su. fahd na fitowa daga motar sukayi ido hudu da atika

gaban ta ne ya yanke ya fadi duk da basufi second 3 ba ama jikin ta yabata wannan labarin idan yaje kunnen hajiya halima za'ayi ta ta kare.

***
"WHAT?! UBAN KUTURU YAYI KARYA WALLAHI!" hajiya halima ta fada da karfi ta suri wani jug na glass ta fita.

umni ce ta zauna da fahd a parlour ta kasa magana se kallonsa take. hannun ta ya rike jikin nasa gam kamar ace

pat!

ta bace.

umni ta bude baki zatayi magana "fa-" se kawai dammm hajiya halima ta bugo kofa.

kan umni tayi gadan gadan hakan yasa fahd yayi saurin mikewa sekuma alhaji abubakar ya tare ta.

gannin hakan se hajiya halima buga jug en da kasa yaba da tasssa. mikewa umni itama tayi duk jikin ta yayi sanyi.

anyi second goma ba wanda yayi motsi se alhaji abubakar ya ja hannun halima suka fice.

masu aiki ne suka fara saurin gyara wurin ita kuma umni ta ja fahd daya karamin parlourn.

sakin hannun sa tayi dasuka shiga ta nufi wani karamin fridge ta bude. "ka zauna bara na kawo maka wani abin ko?"

rintse ido fahd yayi. "umni... kuka zanyi ko daria?" ya tambaye ta har lokacin yana tsaye.

pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now