mijin tsohuwa (3)

678 134 1
                                    

Ajiyar zuciya ya ja yayi salama. Shidai haka allah ya tsara masa baze ji dadin gidan sa ba. A duniya kowa ya sani shi ya tsani hayania amma ba me masa se matar sa.

"Meke faruwa ne?" Ya tambaya yana cire takalmin kafarshi "wannan shashashar yarinyar ce daga ta wanken mayafi ta saka min bleach! Mayafina silk na wurin 100k" ji yayi kamar ya fadi, dan dai dubu dari ?

"Yanzu dai ki kyale ta, zan tura miki kudin" dan guntun tsaki halima taja "ehen se maganar kudi ka dai gama tarawa wasu dan ba me gaje sunanka" ta juya ta shige daki ta barsa a tsaye a wurin.

1) Wanene alhaji abubakar?

Alhaji abubakar adam dan asalin kazaure ne, mahaifiyar wato hajiya fatima su 6 ta haifa kuma 4 sun rasu sauran su 2 shi da yayarshi zainab da ke aure a chan gusau. karatu ne ya kaisa garin kaduna da ya kamala se ya fara sana'a ta business, ana haka ne ya hadu da hajiya halima a lokacin ita kuma tana ss3 da ta karashe karatun ne akayi komi da ya kamata aka daura masu aure . Ana nan ana nan shuru bata taba haifuwa ba kowa yayita mata tsiya kala kala duk tabi ta rame, abubakar ne ya zame mata me jin tausayinta yana tuna mata ae haifuwa daga allah ne, daga baya ya hana kowa zuwa gidan shi sabida baiya son abinda zena bata mata rai. mahaifiyarshi daj ta matsa se an je asibuti. Hakan kuwa akayi koda aka je se likita ya sheda matsalar daga mijin ne.  Ae kuwa nan dangin mata suka tada masifar duniya wae ya chuchi yarsu kaza da kaza. Itama halima halinta ya chanza ba abinda take mashi se bori da tsangwama me namiji kaman mace shidai sedai ya zubamata ido kawai. Duk kowa ya juya mashi baya banda mahaifiyarshi da yayarshi.

If you enjoy this story then tap that ☆ to the left and also check out my other books 😊

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now