Dafara (2)

147 12 0
                                    

shuru tayi se kuma ta fashe da kuka. saurin karasawa inda take yayi rike ta. "ban sani ba nima... ban sani ba"

jikinsa ne yayi sanyi gannin umni na zubar da kwalla. se ya ja na wurin kujera ta zauna shi kuma ya zauna a kasan kujera ya kwantar da kansa a gefen ta.

suna haka har barci ya dauke sa.

***

"Daddy oyoyo" zia ta fada tana murna ta rungume abban ta lokacin da ya dawo. "zia ya zaman gidan?" ya tambayeta yayin da mommy take karban hularshi. "wallahi lafiya kalau daddy. bara na gama shirya table"

girgida kai mommy tayi ita kuma zia ta shige kitchen ta bude fridge ta gama fito da fruits da juice ta tuno ashe betty zata kira ta tayi saurin haurawa sama dakin ta.

wayar ta takai wa suri se kuma ta fada bayan gado. tsaki tayi ta leka karkashin gadon taga wani dan box.

dauko shi tayi tare da wayar tata ta zauna a kan gado ta bude shi.

abu buwa ne data ajiye na tarihi itin wasiku da hotuna a gifts wanda aka bata. tana smile take dudduba wasu a cikin su se kuma ta ga wani note book.

sunan ta karanta gaban ta ya fadi.

"friend....."

ajiyar zuciya tayi ta kwanta a kan bayanta tana kallom ceiling enta.

"ina ka shiga....." ta rufe idonta a hankali

karar wayarta ce ta dawo da ita hankalinta ta mike zaune tare da kiran sunan betty.

***
"na fada miki. ban sani ba" harooun ya fada yana kokarin fita daka ajin. karo na wurin har ya kasa idawa da ake tambayar sa inda fahd yake.

tsaki harooun yayi ya fito da wayar shi sekuma ya mayar da ita aljihu. bashi da number en shi.

"aikin banza fahd!!" ya fada a hankali yau tuesday. ko ina guy ya shiga oho...

Ayush ce ta dan taboshi ya waigo rai a bace. sekuma yayi ajiyar zuciya.

turo baki tayi. "senior fushi kake dani waee" girgiza kai yayi "never. ama yanzu I'm busy" yayi mata wani karamin murmushin da atake ya gushe sekuma ya taba ta gefen ta ya wuce.

"meke faruwa ne?" ta fada tana cika baki a shagwabe. wata me rike mata jaka tace "naji ance fahd aka cire daka makarantar"

tabe baki ayush tayi "duk maganganu ne." setayi gaba mabiya na baya

Pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now