kaskanci (2)

823 60 2
                                    

Gyara zama umni tayi ta kuma karayi masa kallo "wane friend? Na zata kace baka da abokai?" Girgiza kansa yayi ya dago bakin nan kamar ya shafa lip gloss "sunnanta zia. Ita ce first friend ita"

"Okay...a makarantan ku take?" Umni ta kara dai tambaya "ehm" ya kada kai "Thom zanzo na ganta" zumburo baki ya danyi baya so umni ta je ta rufe zia da tambayoyi ama yasan idan ya fadi haka zargi ne ze biyo baya.

Ji sukayi am fara tafka salama "Saalaaamuuuuu aleeeeekum" seda fahd ya dan kware. Umni ce tayi saurin mikewa tsaye "fahd kayi sauri, ka daukomin shijabi na" gyada kai fahad yayi ya mike.

Wata salamar aka kuma takawa amma wannan karon umni ta amsa. Karban shijab in tayi a hannun fahd ta nufi waje.

Malama hansai da danta tasiu ta tarar a woje suna ta cika suna batse wa.

"Malama ina wuni" umni ta gaishe da ita kasancewar ita ayashe ta girme mata. Budar bakin hansai se cewa tayi "gaskiya ba lahiya" umni ta gane ba zuwan arziki bane dan haka bata gaiyaceta ta shiga gidan ba. "Yanzu ace danki! Yana wulakanta babban dana na miji? Ae wallahi ba kiji dadi ba" ta karashe maganar ta cikin tsaki.

"Ban gane nifun naki ba?" Wani mugun kallo hansai ta bita dashi "ehhhh danki muhammadu! Be ci sunansa ba wallahi tallahi. Karami dashi ya fara halin banza! Yanzu ace har ya fara like wa yan matan makaranta ana wulakanta dana?" Hansai ta fada cikin tsawa.

Kasa shuru umni tayi. Duk duniya ba abinda yake bata mata rai irin taga ana musgunawa danta " gakiya ba halin dana bane haka kidai kara binkice. Kuma maganar be ci sunanshi ba ae ba da inkiyar gidanku aka saukar da shi ba" umni ta ce a natse ba tare da daga murya ba.

Ran hansai kuma baci yayi ta kasa magana. tasiu ne ya ara ya yafa "koma menene na gode wa allah ina da uba! Shi ina nashi? Inkiyar gidan mu? shi dan naki da kike ji dashi yayi amfani da tasu? Karshan kaskanci kenan ace an haifi cikin shege"  umni juyawa gida tayi ta banka kofar ta rufe, nan ta bar uwa da danta suna ta tashancin su.

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now