marayan dole (2)

289 28 2
                                    

minoo na tsaye a kitchen tana sanar wa da ma'aikatan shashin yadda ake amfani da wata sabuwar na'ura ta wanke wanke fahd ya ja ya tsaya.

daya da ka cikin masu aikin ce ta kula dashi tayi wa minoo magana.

"ah fahd? har wayar ta kare ne?" ta tambaye shi cike da kokonto. "uhm" ya gyada kai ya mika mata wayar.

smile minoo ta danyi dan ya kawo kansa "zo muje yau sena ga a gaba na kaci abinci"

"uhmm" ya dan bata fuska. ita ma hade rai tayi "kai ma kasan baka isa ka dena cin abinci ba" minoo ta murguda baki tare da sa hannu a kugu "ko ka cinye nan ko wallahi yaro muyi kafurci dakai dan dure zamma na kauye ma kuwa"

ganin dabancin minoo yafi karfinsa ne yasa fahd ya wuce da sauri ya zauna a kitchen dining na staff.

***
bayan shekaru biyu sun wuce
***

Zia ce zaune a gaban mirro enta tana faman taje gashinta.

A yanzu ta cika yar shekara goma sha bakwai a duniya. tana karatu a makarantar Queen's court music dake kasar america.

yau ce ranar asabar take shirin komawa Nigeria ganin gida.

wayar ta dake ajiye a lan bedside ce ta hau ruri. ko da ta dauki wayar bata duba me kiranta ba dan ta tabbatar mommy ce.

"hello- mommy ina kwana?" ta fada tana gyara tsayuwa.

mommy ce ta amsa "lafiya kalau. kin shirya ne?"

kallo zia ta kuma yi ma dakin dake a barbatse ko alamar gama hada kaya be nuna ba "ehmm..." tayi karya.

"thom. dama bana so ayi ta last year dakika je kika yi missing din jirgin"

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now