biyayya ko bauta (4)

529 41 5
                                    

akan meyasa zan na takura wa kaina harhaka. murgina wa tayi ta dau wayar

"salam. ina wuni" ta fada da murmushin da be kai zuciya ba. jin muryarta tayi wani iri kamar wadda akai ma dole hamid ya danyi shuru

"me ya faru" ya tambaye ta. bata tsaya inda inda ba tace "kaina ne yake ciwo" shima be yi wani dogon bayani ba yayi mata sannu sukayi sallama.

tana ajiye wayar ta mike. "yau dai iska ya kamata na fita in sha kawai" ta fada a ranta yayin da take gyara hular kanta.

****
karfe 3:30 na dare

fahd na kwance a kan gado yaji karar knocking a kofar shi. banza yayi da shi kamar yayi barci ya danne kanshi da pillow.

muryar umni da yaji ne ta na kiran sunanshi yasa sa ya mike da sauri ya bude kofar.

kofar na karasa bude wa ta rungumo shi tana shashekar kuka sosai.

idonshi ya bude sosai cike da mamaki jin hawayen umni na sauka akan wuyan sa tana fadin "fahd kayi hakuri... i couldn't give you a good life kamar yadda ya kamata... ka yafe min..."

shima ji yayi hawaye sun cika masa ido. umni... ya fada a ranshi kuka na sauka daga idonshi.

nagode


Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now