marayan dole (4)

306 29 4
                                    

A yanzu haka ma yana gidan mahaifin nashi. tinda yake zuwa so daya suka taba haduwa shi ma zuwan shi na uku ne da azumi

ya tafi masallaci sallar asuba se suka hadu a hanyar zuwa ya tabaye sa akan karatu da dai wasu abubuwan chan da basu dami fahd en ba tinda dama mahaifin sa baya cikin lissafin sa.

dama yaji ana cewa wai baban nashi dan kasuwa ne baya zama wae acewar har abin ya kai ya kawo matar shi bata fi ta ganshi so takwas ko shida ba a shekara.

yau kasancewar ta asabar fahd na zaune a chan bangaren shi da aka ware masa me daki ciki a parlour da bandaki. yana tilawa aka kwankwasa kofar.

dan hade gira yayi sa'annan ya mike ya nufi kofar shigowa ya bude.

"ya fahd. ina wuni!" wata yar yarinya da bata wuce shekara tara ba ta fada da karfi a sanda ya bude.

rintse ido ya danyi dan haka Allah yayi yar nan da karar bala'i. yace "lafiya kalau sha'hida jeki wasa"

turo baki tayi "ni kazo muje wasan tare" shuru yayi mata ya fara kokarin tura kofar "ya fahd yau ya hameeeed zaya dawo fah wai"

a zuciyar shi yace kun ji wata sabuwar kuma. "toh"

"yaya yau mom ena zata zo wurin aunty ma"

se a sannan ya gane cewa ma ashe sha'hida yar ruko ce.

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now