Cin aziki (1)

160 13 2
                                    

Hajiya halima na zaune a parlour tana cin apple atika tayi sallama akayi mata alama da ta shigo.

"hajiya... su Alhaji ne suka fita" atika ta fada tana huci Allah Allah take ta gama amayar da abinda ke cikin ta.

"ina suka tafi"

Kamar abin arziki atika ta fara magana "ae wallahi naga tana ta cin magani tana iyayi shikuma yana bin ta a hankali. shi ne ma yake bude mata kofa"

Wata tsawa hajiya halima ta dakawa atika "KEE Dallah malama ba cikan kunne nace kiyi ba"

"B-ban san inda suka je ba" atika ta fada jiki na rawar sanyi.

alama hajiya halima tayi mata da hannu atika ta tashi simi simi jiki ba kwari ta fice.

wani glass ne na ado akan table en gaban hajiya halima. kallo ta karayi wa abin tayi wata mummunar daria irin ta bakin cikin nan ta sa hannu ta barar da komi na kan table en.

tsaye ta tashi tana kada kai kamar wani kadan gare "lallai ne abubakar. wae kai dan love ko? ka zama maye kana bin wacen yar iskar kenan. ni gani shegiya an ajiye ne"

kwafa tayi ta dora hannu a lan kugun ta. wallahi badai ni ba... babu dan shegiya wallahi!

***
kwanan zia hudu da dawowa sukayi da hameed zasu hadu. dama duk da basa magana kamar da su a cewar su wae tsohuwar zuma.

ta sha kwalliyar ta cikin kayan hausa ta nada daurin ta. tana shafa janbaki tana rera waka a harshen turanci ita kanta ta san sautin ta da dadi.

kiss ta hura wa kanta a mirro ta karewa kanta kallo. ta kara tsaho da kyau sosai. dama tinda ta je ta bar ranar garin nigeria fatar ta se wani fresh take yi.

purse enta ta dauka tare da wayar ta wadda ta saka sim Airtel aciki ta wuce kasa.

mommy na zaune a kan dinning ita da jabir zia ta taho chul chul da hills enta itama ta zauna tare da su.

"kedai kamar wata chokali, mitsweee stupid kawai" jabir ya fada tare da maida hankalin sa kan damun shinkafar da yaji kayan hadi ya gaji.

turo baki tayi. "mommy zani waje na sha iska. zamu hadu da wani friend"

***
pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now