jarumi (3)

573 59 2
                                    

"Fahd!" Safyanu yakira sunanshi se kuma ya tsaya yana kafkafta ido kaman mara gaskiya "ba malama ce take kiran ka ba.... kar kaje ko hanyar office" yana gama fadan haka ya juya ya bar fahd a tsaye yana mamakin hali irin na mutum

A bayan office.  Dayake makarantar babba ce sosai kuma tana da arzikin bishiyu yasa ba lallai ne a san meke faruwa a bayan ajujuwa ba da sauransu.

"Dan yar mara mutumci! Baza ka kirashi ba kenan?" Ingozi ya dura ashar yana yarda guntun tabar da ke hannshi. "Wallahi bashi da baba kuma kunsan idan wani abu ya same shi mamanshi zatazo! Dan allah ku kyale shi" safyanu ya fada cikin kuka. "Mitswee" saminu ya ja wani dogon tsaki ya daga kafa iya karfinshi ya takawa safyanu rowan cikin shi seda ya kifa yana kakari. "Wanene ya tambaye ka? kawai muyi manegi"

"Eh kuwan" idi ya kyalkyale da daria ya fara kokarin zamewa safwanu wandon jikinshi."idi rike min shi mna-"

Fassssssss!! Kuke ji karar balewar katako a bayan ingozi, dif ya sulale sume a take a wurin. Hakan ya jawo hankalin su saminu da idi dake kokarin zame mawa safyanu boxers kan fahd da ke tsaye a kan ingozi dauke a kafar kujera irin stooll enan na malamai me kauri.

Tunawa da baya
(Flashback)
.
.
.
.
.
.
A lokacinda baba mahmud ke goge masa ciwon dake fuskarshi ya ke gaya masa "kasan marabar namiji da jarumi?" Fahd ya girgiza kai yana dan rintse ido sakamazon radadin rubbing alcohol en da aka kara a ciwon shi. "Namiji shine wanda yake dan adam kuma ba mace ba kuma yake baligi me kula
da zuriarshi shine cikarken namiji..."

Karshen tunani
(Flashback ends)

A lokacin da safyanu ya dawo hankalinshi gaba dayansu ya gani a kwance a sume. Yaji an miko masa hannu ya daga kai

Shikuma jarumi shine wanda yake wa jama'a hidima...koda shi kanshi baze samu komai ba komai tsananin bala'i....

Nagode voters

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now