binkice (4)

668 53 0
                                    

"Fahd shiga ka kintsa kazo" umni tace rana shafa kanshi gyada kai yayi ya shige daki.

Hajiya amina ta zuba musu ido, kwata kwata bata ga alamar abun da hansai ta fada mata ba.

Ba a wani dade ba ya fito kayanshi a wanke a goge tsaf ya samu wuri ya zauna a kusa da umni.

"Su nanshi Muhammad ko?"

"Eh"

Juyo da hankalinta hajiya amina tayi gun fahd "mesa baka zuwa iskamiya?" Shuru yayi kaman baze magana ba yace "na sauke littattafan"

" thom yi min adduar da ake idan anga danyen dan itace?" Hajiyabta jefo masa tambayar kamar daga sama

Allahumma baarik lanaa fee thamarinaa , wa baarik lanaa fee madeenatinaa wa baarik lanaa fee saa'inaa, wa baarik lanaa fee muddinaa.

Ya amsa mata kai tsaye shima. Haka tabi tayi ta tambayansa akan addini duk ya bata amsa.

Shuru tayi... Ta fahimce hansai gero da dawa ta hado mata. "Thom allah yayi maka albarka." Umni ta ce amin shiko se raba ido yake

Islamiya umni keson saka ni ne?

"Fahd abincinka na kitchen" thom ya ce ya mike yayi tafiyarsa. "Nafisa... A gaskiya ina shakka akan abin da aka gayan...ama ina mahaifinshi yake? Nasan dai bazaki iya sabon allah ta wannan munanniyar hanyar ba"

Shuru umni tayi tana kallon kasa. "Menene sana'arki?"

"Ina hada turarukan kamshi kuma ina yi ma wata mata a bayan mu aikin gida"

"Nawa kike samu a wata?"

"Wataran idan na hada yana kai 8900"

Bata fuska hajiya amina tayi "yanzu maryam idan ya gama secondry ya zakiyi dashi? Kuma ba fata ba idan wani a cikin ku ya kamu da rashin lafiya fa? Bashi zaki amsa? Idan baki samu bafa?" Dan sanyaya muryarta tayi ta cigaba "kizo gidana kina tayani aiki. Ba wani abu me wahala bane kawai shara da moping ne. zan na biyan ki dubu hamsin duk wata"

Na gode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now