Cin arziki (4)

206 19 10
                                    

kici kicin kwacewa ya farayi ama karfin sa be zo ko rabin na rock ba.

"Alhaji meye ya faru naga kamar zaka fadi" rock ya fada a hankali yana kokarin jan fahd wurin motar

gannin za'a iya gano su yasa rock ya fara kokarin shaka masa wani kyale a hanci

wani bakin ciki ne ya dunkule ya tsaya a wuyan fahd. ji yake wani irin jiri hade da ciwon kai suna kwashe shi

saurin sakin sa da rock yayi lokaci guda seda ya firgita sa. da sauri fahd ya matsa baya har yana faduwa. kallon yayi da yake dauke da murmushi a fuskar sa. juya wa yayi yaga wani mutum na tahowa.

wani irin kallo me cike da tuhuma ya harbawa rock kamin ya huyo kan fahd. ritsinawa yayi ya taya fahd mikewa "mene yake faruwa haka"

"Um...umn..." so yake yayi magana ama ya kasa se kuma amai.

da sauri rock ya fara bayani "kansa ne yace yana masa ciwo shi ne zan kai shi asibiti"

dagowa fahd yake kokarin yi dan ya kalli idon rock se kuma amai yakuma taso masa.

Alhaji Abubakar be bata lokaci ba ya suri fahd, hakan be masa wahala ba kasan cewar shi yana da karfi sosai a jikin sa.
***

"Hajjo ina wuni" umni ta fada tana ritsinawa. murmushi hajjo tayi "lafiya kalau. naga baku shugo tare da me gidan naki ba kuma"

waigawa umni tayi "eh. bara in shigo dashi"

tana fita taga yana rufe sit en baya da sauri. itama kawai ji tayi ta suri kafar ta ta shige motar.

kamar irin kidnappers en nan na film tana shiga ya ja motar suka bar gidan.

tana leka bayan sit taga fahd a kwance ya rike kanshi. aiko a hargitse ta haura sit en bayan.

"fahd... meya same ka... ni ce ka gane ni? umni ce" ta karashe maganar muryar ta na rawa.

a hankali ya rike hannun ta yana kokarin tashi ta maida shi. zuwa yanzu har sun isa wani nearby privet hospital.
***

likita ne ya fito da takardu a hannu ya farayi ma Alhaji Abubakar bayani "he is exposed to a certain amount of chloroform."

wato ya shaki chloroform wani abu ne da ake sumar da mutane da shu amma har kisa yanayi abun.

Shuru Alhaji Abubakar yayi se ya ce "yanzu a'a iya shiga a duba shi"

gyada kai likitan yayi suka gaisa yayi gaba

pp-panda

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now