rayuwar mu (2)

508 42 1
                                    

"Da wannan matar"

Halima.

Shuru yayi yana kallonta. Ta ci gaba "ko ka sake ta. Ko kuma ka kara aure" hannu yasa ya dafe kanshi "ya Allah. Kin fi kowa sanin hakan bazai yiwu ba"

"Salama alaikum" ta shigo da tray me dauke da kayan tea ta ajiye musu akan center table tayi serving ensu sannan ta juya ta fita da sauran.

Ajiyar zuciya hajiya zainab tayi "karya ne. Ni nasan lafiyar ka kalau, su ne chan da matsala" ta ajiye cupin hannunta ta koma gefen shi ta zauna tana dan bubbu ga masa kafada.

"Inaso kayi tunani... ko badan ni ba? Please?"

Gyada kai yayi ya danyi yake. "Zan koma daki" bata yi kokarin tsayar dashi ba tace "thom. Nasan kana bukatar lokaci?"

Washe gari ya fara shirin tafiya dan daman wani abu ya taso a company enshi.

A cikin yaran hajiya zainab ba wanda yaji dadin hakan ama sunyi alkawarin kuwa da hutu tinda daman exams ake.

Yana cikun tuki akayi masa waya. A driving mode yasa wayar ya daga. "Salam alaikum?"

"Mitswweeee..." aka ja tsaki ta daya bangaren "kaman gaske. Dama sanar ma na kira enyi. Na fasa dawowa se new year. Ka turon wani abu da zan rike a hannu"

Ko ba a fada ba yasan wace kawai ya katse wayar. Ya fara considering din abin da yayar shi ta gaya mae.

Nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now