kadara ce (4)

484 43 13
                                    

ringin daya biyu minoo ta dauka.

"salam. minoo?' kin gane me magana?" "eh. umni ina kwana?"

daka kan dining umni ta tashi ta koma tsakiyar parlour ta tsaya tare da gyara rukon da tayi ma wayar.

"lafiya kalau. minoo... dan Allah hada ni da fahd?" thom minoo tace mata se kuma ta kashe wayar.

wata royal cushion umni ta samu ta zauna. tinda aka kawo ta gidan bata taba sa me gidan nata a idonta ba. ko bakin kofa bata taba fita.

kullum kamar hoto ita kadai se dai yan aiki masu zuwa su gyara wuri su tafi.

da kayan kallo kamar me ama kwata kwata basa gabanta abu uku ne suke mata yawo aka.

wane hali fahd yake ciki? waye me gidan nata? ko ze barta tana haduwa da dan nata?

kallo ta karayi wa parlourn. gaskiya an zubar da kudi sosai dan kowane furniture royal ne me tsada kamar mafarki.

tagumi ta tafka ta kura wa sabuwar wayar ta ido. ba abinda ta zo dashi cikin gidan. har kayan da tasa ranar da aka kawo ta ma dangin mijin nata ne suka tanadar mata.

umni na chan wata duniyar bata ji sallamar da akayi ba. har ya gaji ya shigo idonta na kafe kan wayar.

nagode

Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now