yaa fahd nake so (3)

543 41 14
                                    

***
wani irin sarawa kan zia yake sanda ta farka daga barci.

a kan jirgi take zaune a first class. wata attendants ta tsayar ta tambaye ta "shin wai sauran minti nawa mu isa abuja?"

da fara'ar ta flight attendant en ta tace "befi sauran hour biyar ba"

tsoka zia tayi "yi tafiyar ki"

"tsokana ko?" wani dattijo da ze iya yayan babanta fada cikin murmushi

girgiza kai tayi "uhm uhm. ina wuni?"

"lafiya kalau" ya amsa cikin fara'a

***

a cikin dabi'un da umni ta dora wa fahd akwai son saka safa komi yanayin garin. ya dauko wasu black kenan yaji karar motoci. suna shigowa harabar.

ji yayi gabansa yayi wani munannen faduwa. hannu yasa ya dafa kirginsa

a gefen gado ya koma ya zauna yana kokarin zura socks en shi dik jikin sa ba dadi.

anyi haka da awa uku an idar da sallar magrib yana komowa gida yana wuce gate ya ga wasu mata sun taru a jikin wata ash colour en mota suna ta shewa.

be tanka ba ya raba ta gefe inda ba me kula dashi yana kokarin karasawa shashin sa yaji ana kiran sunan sa.

"Fahd!"

dakatawa yayi ya juyo nan yaga me kiranshi. a take ya gane fuskar shi dan ko a mafarki baze taba mantawa da itaba.

"guy bamu haduba ko? sunana hameed. your brother" hameed ya gama fadar hakan ya mikawa fahd hannu su gaisa.

"sannu da hanya" fahd ya ce shima suka gaisa "paps yace mu zauna a side enka tare sabida.. ai kagane ko?"

gyada kai fahd yayi.

a zuci yace kai ka rabani da friend...

"zo kayi meetin en abokaina mana" hameed yayi masa nuni da tarin matan dake ta daria suna shewa a gefe. "gani na suka zo yi"

kasa shuru fahd yayi yace "su nawa?"

wata daria hameed yayi "ni har na manta yawan su ma wallahi"

murmushi fahd yayi a fuska ama ya dunkule hannun shi yayi kamar zai wata maganar se kuma bakinsa ta kasa budewa

ya gyada kai ya juya ya cigaba da tafiyar shi.

ita zia fa...?



Shahara (Hausa Love Story)Where stories live. Discover now