Aure II

209 7 0
                                    

Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by J Hajara

2️⃣1️⃣&2️⃣2️⃣

Oga yace" tsoho"

yanuna Wanna tsoho da ya ma Aliyu  magana ..yace

" Kai zakazama waliyishi" "Alhaji" yakira Daddy karami "Kai Kuma kaine waliyita "

Aliyu yadaga Kai Yana kalloshi yace" ikon Allah bara na ga ta ida za 'a ma mutum aure dole "

Daddy karami naji haka ya Soma jijiga Kai Yana hawaye ya rasa tacewa, Essha ma hk fuskata kife a cinya Daddy karami tana furta duk addu'a da yazo bakita..

Hajiya tagama rikecewa lamari ya girgiza ta, sai kuka tace" Allah sarki Essha Allah na tare da ke aure ba shiri, yaro  bamusan danga inda ya fito ta share hawaye tacigaba " bamusan dangishi ba ya Allah kaine gatamu ka kubutar da mu daga hannu azaluma bayika na ya Allah".. ta juya ga kallota ga Essha ta sake kallo Aliyu tunda ga samashi har kasa ta girgiza Kai tace" ohh Allah na Kai kasan yadan kake ikonka,  Allah mu gode ma, ya Allah gamu gareka , ka karemu ya Allah ".. yariya karama dake gefeta ta amsa da ameen itama Tana kuka, hajiya ta rugumeta ..

Aliyu yakai dubanshi ga yariya da hajiya ta rugume yace" ba dai yariya na bane suke magana za su aura min, subhanallahi Wana ai ko sa'a su Sofia Bata Kai ba "...

Oga da hankali shi duka Yana kan Aliyu dake kallo su hajiya yayi murmushi ya kadan Kai a ranshi yace" da alama dai tausayisu tsohuwa na ya kamashi"

yayi kwafa .."zanyi maganika ai, Kuma da su zanyi amfani guri maganika Naga Alama tausayi su a idon ka" Yayi murmushi yace" Kai kurmo kuje ku dauka motar Dan samari nan"

Kurmo yace " toh rankashidade "

ya fice ya je ya turo motar har ciki daji ..  Aliyu kallo mamaki kawai yake binsu da shi.

"Tsoho amatsayi ka na wakili ango ,toh sadaki zaka dauko aciki motar na , ko nawa ka gani ka dauko" oga ya fada Yana kallo tsoho .. 

Baba tsoho ya Mike jikishi na Bari ya kalli Aliyu   .. Aliyu ya lumshe minshi idon Alama yaje ba matsala.

Yana Kai baki motar yarike handle bude kofar motar yakasan budewa don jikishi yakasa natsuwa kadawa kawai yake.  Kurmo yasa key din ya bude minshi , Yana shiga ciki motar ya ji wani sanyi kamshi na tashi ya duba ko'Ina ciki motar baiga kudi ba yafito still Yana Bari yace" Rankashidade ba komai aciki "

Daddy karami sai binsu kawai yake da Ido ga Essha takiyi shiru..

Oga yace" kubude mishi baya boat yaduba". . aka bude minshi, trolley dinshi ne, sai extra tyre da karfe gyara tyre ..  yayi dauriya yasa hannu a trolley ya bude karami zip  din ,   bandir bandir din pounds yagani, ya matukar firgita dun tundayake bai taba gani kudi haka a zahiri ba. A hankali ya sauke murfi boat din, jikishi na Bari ya nufi guri oga,, har kasa ya durkusa ya mikamishi.

Aliyu yace " waiyazubillahi 🤦 kaico, waena mutani Basu da Imani". ...

Daddy karami da Hajiya kansu na kasa Basu iya kallo su ba don takaici da bakiciki .

Baba tsoho na Mika ma oga kudi yayi mamaki dagani bandir din pounds 💷, don shidai bai sata ama duk abubuwa da sukeyi bai taba gani pounds ba , sai dai sugani a tv.. a zuciya shi yace" lallai Wana yaro Tycoon ne"

yace" yo ai tsoho Kaine waliyishi , rike don sadaki Matarsa ce da zai aura, saboda haka.... .."

Aliyu ya katseshi  yace" what the heck did you mean by that?Eeyeh zai zama waliyi na baya basa Shiba, ku Wai waensu iri mutani ne marasa Imani da tausayi"

Oga yayi dariya yace" Ina na zuwa kanka tukuna, tsoho gayamishi ko Kai waye?

Baba tsoho na abun tausayi yajuya ga Aliyu murya na rawa yace" suna na MALLAM DANGANA daga TATARA  nine limami gari"

Oga yayi dariya ya harba bindiga a sama yace " yawa yazo a daidai, toh Dan samari kaji dai sunashi dakuma inda yake , toh sai ka gayama na naka suna , dun za' a daure aure ba Bata lokaci"

Aliyu yace" what! Toh bazafadaba " ya fada cike da baci Rai ..

Oga yayi dariya yace" Dan samari matsala na dakai tauri kai , zaka fada ko baza ka fada ba ?"

Aliyu ya hada fuska tam yace" eh bazan fada ba " ya kau da Kai , Yana kau da Kai suka hada Ido da Daddy karami,na take Aliyu yaji shakkashi ya kamashi yayi sauri sukunyar da Kai..

Oga yace "  na yima wani alkawari ana ba za cutar da Kai ba, ama nakusa da Kai ne zasu Sha wuya kafi a daura aure na".. Aliyu ya daga Kai ya kalleshi baice uffan ba..

" Kai Reza sama tsohowa wancan bindiga" yanuna hajiya  yace" In na kirga daga daya zuwa goma bai fada ba ku harbeta, Kuma na tabatar minshi aure dole sai an daura da ESSHA"

Essha naji hk ta Mike daga jiki Daddy karami , Daddy k shima ya razana yarasa abunyi , kuka kawai yake kamar Karami yaro, yau shine Hajiyasa za' a kasheta a gabanshi" Kai duniya .."

Hajiya naji bindiga akanta tarasa na cewa, sai Bari kawai take a zaune ga bindiga kanta tana kallo Aliyu ..

Aliyu shima ya razana matukar razana"yanzu akan bafadi sunana ba shine za'a kashe Rai ,ah ah banzayi kuskura danayi datzu ba, wait toh wacece Essha" ya tambayi kanshi?

  Bai Gama rufe baki ba Essha ta wuce taganbashi , ba daukali akanta, gashi ta ya rufe mata rabi fuska..Nan yaji..numfasa na nema daukewa, yabita da kallo har ta karasa gaba oga ta rike minshi  kafa tasoma magana a murya kuka" da Allah Kar ka kasheta , da Allah na rokeka .... "

Aliyu daji murya ta yaji wani abun ya soke shi a kirji Nan take ya rike Sai gurin ,kirjishi sai duka uku uku takeyi yarasa dalili, sai bin bayata kawai yake da kallo Yana son yaga ko wacece hk ke neman halakashi..

Oga yayi dariya yace" Essha na samo Miki Miji amafa Dan tauri kai ne,da alama baison taruwa dangiki ne kafi aure..."

Nan take takara ji faduwar gabata ya tsanata .. ta tsikoyo murya ogan nacewa" daya, biyu ....."

Aliyu kam duk bidiri da akeyi na ceto hajiya hankali shi ma ba ya wanjan. Yayi zurfi a tunani yariya da tafi da Imani da nutsuwarshi ..

Oga yacigaba " uku" Essha takara rike minshi kafa tace" yallabai da Allah Kar ka kasheta na rokeka "

Ya amsa da cewa" yariya bani Zaki rokaba, angoki Zaki roka , dun Naga Alama baison gani kakarki da Rai, gashi can"  yanuna Aliyu yacigaba da kirga "hudu "

Ai Essha da sauri tabar gabanshi ta nufi guri Aliyu , dun har tayi tutunbe zata fadi .. Aliyu yayi sauri tareta ta fado a hannushi .. Essha kirji ta sai bugawa yakeyi kamar  zai fito, Aliyu  ya tsaya shiru Yana kallo ta Ido ciki Ido..

Ya lumshe Ido ya budesu " tsarki ya tabbata ga Allah"

shine abinda yake fadi a zuciya shi "  sanan yace"  love at first sight pretty " ... Da sauri ta kauce kata daga hannushi  tana Bari , shikam ma ya kasa motsi , yariya ta tafi dashi , Essha nata magana baijitba dun wanna hklishi yayi nisa,baya  Kuma oga har yakai shida a kirga ..

Da karfita tasa duka hannuwata ta girgiza shi tace" bawa Allah bakajina ne zai kasheta da Allah Kayi magana Kar ya kasheta ka fada musu sunaka , badai aure bane, andaura shikena ama da Allah Kar kabari su kashe min hajiya " ..tana magana tana hawaye ..

Aliyu kam yayi nisa fuskata da yanda labeta suke motsi kawai yakebi da kallo..

Oga yace" takwas " da karfishi  .. Reza yakara gyara kunama bindiga yayi kakas kas yayi ready harbi ..

Daddy karami  sai  kuka ba dama ceto..

Essha tace" wayyo Allah zasu kashe min ita, Wai mallam bakajina ne, ka fada musu sunaka please please karsu kasheta " takara fashewa da sabo kuka ta kifa Kai a gwiwarshi tana jijigashi .. jiki Aliyu kam yagama mutuwa

Oga yace" Taraaaa"   da sauri Essha ta daga Kai ta kalleshi yasa hannu ya yaye mata gashita da ya rufe mata Rabin fuska, ita kam haushi da tsana shi takeji wani matsanaci tsanashi takeji ta rasa dalili .. oga zai bude baki kenan yace goma ..

Aliyu ya kalleta idon ciki idon yace" sunana Aliyu Umar " ya furta a hankali

Juma'at Kareem 🥰💃



Comment & share🥰🥰♥️

DOCTOR EESHA👩‍⚕️حيث تعيش القصص. اكتشف الآن