The pics

228 9 1
                                    

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
     *DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

  *WRITING BY*
*J Hajara*

🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️

      *M. W. A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

 
8️⃣3️⃣&8️⃣4️⃣

"Wayyo Allah na... Yanzu in Daddy yagan hoto na Mai zan ce mishi.. ni dai kam na banu gaskiya am not happy with the person da ya dau hoto na"  cewa Essha da keta fama Safa da marwa a daki..

Ta nemi guri ta zauna a bedside tana tuna incident din.. abun ma dariya ya bata can karshe makwashita ta furta"Mad guy" tana dariya..

Taji budewa kofa an shigo da sallama.. ta dago ta amsa ... Mufeedat ce ta shigo.. ta karasa gefe ta, ta zauna tace"Sis Essha Mummy na kiraki..that you should go and have your  dinner"

Essha ta Bata fuska tace" No ni na koshi"

Mufeedat ta Mike tace" zanje nagayama Mummy cewa kice baza ki ci girki taba" ta fada Tana tafiya..

Essha ta Mike da sauri ta kamata tana dariya tace" Autar Mummy dun kawai nace na koshi shi ne harda shairri"

"Eh mana.. Mummy tace tasanki.. tun abinci safe baki ci komai ba..so ki zo muje ki ci abinci ko naje na fada Mata kince baza kici ba"

Essha ta ja Mata kumatu tana dariya tace" yanda kike zakewa na..nasan ba Mummy ce tayi girgiki ba..ke ce ko.adai dai kenan toh bazaci jagwal ba ehen" cewa Essha.. ta koma gado ta kwanta..

Mufeedat tayi rau rau da ido zatayi kuka tace"Sis saboda ke fa.. yau nayi kirki shine kince baza ki ci ba toh zanje na hadaki da Daddy" ta fashe da kuka ta bude kofa ta fita..

Essha ta sauko  da gudu ta bi bayata tana"am sorry little sis yihakuri, kawai na loosing appetite ne shiyasa but zanci kiyi hakuri"

Mufeedat ta ja ta tsaya.. har Essha ta karaso wurinta. Ta Bata hannu su ka karasa wurin Dinning..

Ta zauna mufeedat ta serving nata Tuwon shinkafa miyan taushe. Kadan ta ci ta mike..

Mufeedat dake tsaye gefeta tace" Sis badai ki koshi ba?

Tace" Eh autar Mummy na koshi, let's go"

Ta ja hannuta zuka fito zuwa main parlour inda suka tarda Family zaune suna kallo .. Essha ta nemi guri ta zauna gefe Mummy ..

"Kinci abinci kuwa? Mummy ta tambayeta..

Tace"Eh Mummy naci"

Mufeedat tace" Mummy kadan ta zakula ta tashi"

Mummy ta kalleta, ciki sauri tace" Allah Mummy na koshi , around 5 fa naci Snacks da Malt am full Allah Mummy na koshi"

Mummy tace" toh naji Essha, ya Office din?

Ta amsa da"Alhamdullilah mum"

Mummy tace" badai matsala bako?

Tace"Komai normal mum, naji dadi aiki a wurin"

Mummy tace" toh MashaAllah, Allah ya taimaka"

Ta amsa da ameen..

Nan suka cigaba da kallo film din ama badan Essha da ta fada duniya tunani..

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now