Rabuwa

184 6 0
                                    

Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by-j-hajara

2️⃣4️⃣&2️⃣5️⃣

Kanshi na kife akan kirjita tana bishi da kallo sai hawaye kawai ke fita, taji duk duniya  bawanda ta tsana kamar shi, ta turashi gefe da karfita, tanason ta sauka ama inaa takasa ,tana gani jiri gashi Kuma kasata kamar a babaketa ta daurai ta dauki abaya ta ta saka, Daker da cije lebe ta sauka daga kan katifa , da rurufe ta fito daga bukka tana gani jiri gashi idonta har wani dishi dishi take gani, tana fitowa ta hango su hajiya nesa da ita kadan su zuba tagumi da alama dai ya kungiya su wunce. Tananso Kira hajiya Ina bataiyaba magana ma bai fitowa , sbd murya ya toshe don kuka.. sai daga hannu takai ama basusan matayiba.. kamar ace ma baba driver ya daga Kai ya hangonta tana ta daga hannu a zaune Tana haki ,  da sauri ya sanar ma su hajiya, ai a dari suka karasa gunta... Suna karasowa ta Suma a hannu hajiya , daddy karami  a dari ya sugumeta har guri motarsu, hajiya da baba driver na biye dashi, ko ta kan Aliyu basuyiba,  daddy karami dakanshi ya zauna a mazauni driver ya kwashe a guje sai lafia..

Kurmo ne labe a baya bukka yana gani wucerwasu daddy karami ya fito daga ina yake labe , Ashe tun lokaci Dan yan kungiy su ka bar guri bai bi su ba, ya labe a baya bukka, Yana fitowa sanda ya duba gabas da yamma, gudu da arewa bai ga kowa ba, sanan yasa Kai a bukka...

Aliyu ya tarar shabe shabe a kan katifa da jini a jikishi kamar anyanka karami kaza, kurmo yayi sauri kauda Kai , aranshi yace" yallabai ka yafeni, ka taimakeni a rayuwa ama ni na kasa taimakoka" ya fada Yana share hawaye , ni nasani ai dole tablet Dina yamishi illa har hudu fa .. daga yau  nabar kugiya na inshallah , zan cigaba da rayuwa na yanda Allah ya ajeni" .. ya juya ga Aliyu ya tabashi yaji baya numfashi, ya matukar tsorata , ya jijigashi yaji yaji baya motsi, jiki na Bari yace" kodai mutuwa yayi " da sauri yasa kunneshi a kirjishi yaji zuciyashi na bugawa yace" Alhamdullila  bai mutuba" .. ya dagashi ya San mishi kaya, duk kayan ma su baci da jini daga riga har wandon gashi tundama farare ne.

Kurmo yace" toh yanzu yazanyi dashi na shiga ukuna , nasan fuskarshi bamai boyiwa bane dole sai a tsareni da tamboyoyi, ya illahi , toh Mai zan ce musu ? Ya tambayi kanshi.. wata zuciya tace kawai ka daukeshi a motarshi ka ajeshi a gate din gidasu a dake kaduna kawai, ko kama ka ka.. yace yawwa haka za'ayi" ya kalli Aliyu yaga yanda jini yabata mishi riga dakuma digo digo jini a wando , yace toh a hanka zan tukashi jikishi da jini? In police su ka Kama ni a hanya shiga kaduna yanzanyi.. wayyo Allah na " ya dora hannu a Kai yace" Allah sarki gani Wana jini haka nasan yariyana ba Karami wuya Tasha ba" ya kalli Kaya dake .. crazy ne jaga jaga tunda kan riga har wandon kamar wani sabon mahaukaci jikishi .. kodai nasa mishi nawane " ya tambayi kanshi .. ya girgiza Kai yace" Kash bazai ma shige Shiba ,kawai baranayi kasada  na tamaiki bawa Allah na , gaskiya kungiya na, na barshi kenan har abada abada" ya sukuce Aliyu ya sabashi a wuya , har baki motar Aliyu , yaci sa'a motar a bude take , Kuma key ma na jiki motar , ya bude yasa Aliyu a back sit, ya tsaya ya kalleshi shiru , shi gani jini Nan ke daga mishi hankali , ko yansanda su tareshi ya rasa wani amsa zai Basu , ya duba agogo hannushi yaga har uku na Rana tayi , ya daga hannu sama Yana cewa" ya Allah na tuba na tuba ka tabani da gani masu khaki a hanya ya Allah na rokeka " ya shiga ya zauna a mazauni driver ya tada motar sai ciki kaduna, ya na driving Yana ta addu'a aciki ranshi Allah yasa Kar ya hadu da masu khaki ..  Allah kuwa ya amshi addu'a shi, don har yakaraso ciki kaduna har anguwasu ummi bai hadu da security ko daya a hanya ba.. Yana isowa can nisa da gate din ya Parker motar , yadaga Kai yakalli gida yace" Allah na gode ma , Wana gida haka kamar aljanna duniya"  ya sauka ya duba koina  baiga kowa ba , ko Ina shiru shiru dayake anguwa manya ne ,  ya kalli  wani babba masalaci dake gefe gida yace" ko a masalaci na zan ajeshi .. Kai aa bai dai tsarki , kawai zabarshi ciki motar " yazo ya tsaya a window backsit Yana kallo Aliyu yace" yalabai kayi hakuri , iya abunda zaniyama kenan nasan Ina Kai ka asibiti kamani za'ayi , Allah yasa agaka da wuri nabarka lafiya ".. ya juya yabar guri da gudu kamar a koroshi, ya mata yabar motar a bude , Aliyu kam ko motsi ma bayayi balle yasan abunda akeciki..

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Место, где живут истории. Откройте их для себя