Itace

242 9 0
                                    

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
*DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

*WRITING BY*
*J Hajara*


🌍 *MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚 🖊️

*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
__________________________


*Happy Eid in Advance* *lovely Readers🐏🐑* 🐏🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

7️⃣1️⃣&7️⃣2️⃣

Idrees ciki sauri ya bude fridge ya dauko bottle water ya balle ya Yayafa Mai, Aliyu ya sauke ajiye zuciya, ya bude ido a hankali yanaji jikishi Kamar ancire Mai wasu Kaya Mai nauyi, ya Rika Kai Yana sallati.. can ya Mike ya zauna a firgice ya rike hannu Mami ciki tashi hankali yace" Mami kema ki ganta ko?"

Mami tace" Aliyu are you alright? Wa nagani ?"

Yace" Mami Essha Essha I saw her"

Yashiga bin parlour da kallo yaganta can baya Daddy ita a dole buya tayi..

Ummi ta tafa hannu Tace" ohh ni yarsu, Wana aljana yaushe ta dawo ne ? Bamu da labari"

Aliyu yayi banza da ita ya, ya Mike yana mikewa yaji jikishi Kamar ba nashi ba ya mishi sakau ya Soma takawa a hankali ya nufi baya Daddy, Mami duk suka binshi da kallo.. Yana kaiwa ya jawota har wani shock sukaji a take lokaci da hannu su ya hade..

Daddy ya kallesu murya na rawa yace" Wai maike faruwa ne?"

Ba Wanda ya amsa , su ma kansu a rikece suke..

Essha sai kokari fisge hannuta tashigayi ta kasa dun ba karami riko ya mataba, karshe ma da yaga ta turje Taki binshi, kawai gani tayi ya sukuceta kunya ya kamata sosai.. tana ta fisge fisge zata sauka Aliyu yakara rugumota sosai bai direta akoina sai agaba su Mami.. Ammi sukasa fahimta komai hartasoma tambaya kanta Badai Wana bace Essha din? Ashe toh ba aljanabace, in dai hakane toh mu tabka babba kuskure. Sadik Dan Aliyu ne ama Wana Abu da mamaki yake..

Essha kanta a kasa duk kuka yaci karfita takasa ko da motsi ne, gashi kanta ne ya barbazo gabadaya ya rufe Mata fuska, dun gyaleta ya Dede da faduwa..

Aliyu murmushi kawai yake zubowa yanaji wani sanyi a ranshi yau gashi ga preety shi, har sujjada sanda yayi Yana gode ma Allah..

Suhaima a matukar tsorace take sai wani gagwale Ido takeyi kamar a Kama kwarto..

"Wai Aliyu wani dramer ka ke neman hadawa ne? Who is she?" Cewar Mami.

Aliyu bai amsaba Essha kawai yake kallo sai hamdala yake, ya Soma binta da kallo from head to toe Yana murmushi, Essha shi is now a full woman, Figure 8 ya fada a ranshi Yana shafa gashi kanshi.. ya kalli yanda gashi kanta ya rufe Mata fuska gabadaya yanda take kuka, sai ya tuna da lokaci auresu, shima yaji wani haweye yazomai da sauri ya share yaji murya Ummi na cewa" Wai gadaga lafiya ka kuwa, Aya ba sake dawuwa tayi ba musan mataki da zamu dauka?

Aliyu ya kalleta yay murmushi uffan baice ba ya tako ya isa gaban Essha yasa hannu ya yayye Mata gashi da suka zubo, ya kalli fuskar ta, idonta a kulle suke gam, haweye ne keta ambaliya kamar a balle famfo.. "

tabbas Essha din shi ne, subhanallahi she got such a beautiful eyes"
Aliyu bai ji dadi ganita tana hawaye ba cike da damuwa ya dago fuskarta, Essha ji take kamar ta buge Mai hannu dun haushi takeji ama ina duk ta tsorata gashi kunya ya guri take.

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now