Rayuwa kenan

175 5 0
                                    

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
   DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara

🌍 MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚 🖊️

Kungiya d'aya tamkar da dubu. masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta.🤙🏻
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
____________________

3️⃣5️⃣&3️⃣6️⃣

Ya share haweye Mai dumi da suka zubo mishi, ya nufi daki da aka kwantar da Essha,Yana kaiwa baki kofar suka ci karo da Daddy karami da haryanzu kuka yake, daddy ya kalleshi duk ya hargizai yajashi gefe suka zauna a kujeru da aka jera agefe dakuna.  Baya su zauna. Daddy ya kalleshi yayi ajiya zuciya yace" yakamata ka daina kuka na haka duk abunda yasamu bawa mukadarine daga Allah, yanzu kawai munjira farkawata"

"Yaya kunya hada Id......"

Daddy ya daga mishi hannu yace

" ya'isa haka, Kar ka Manta fa duk abunda yasamu bawa haka Allah ya rubuta mishi, ni musulmi ne kaima haka, Kuma duk muyi Imani da kaddara, Ina Kara godema Allah ba keta mata haddi sukayi ba, aure suka hada rokona ana shine Allah yasa ya zamto alkhari, idan da rabo za su hadu tom, dun ace Matar mutum kabarisa, fatana Allah yaba Essha lafiya da hakuri juriya"

Daddy k ya amsa da ameen yaji dadi kalamai daddy, sukara kwantar mishi da hankali, suna zaune suyi jungum sanda aka Kira sallah magarib suka Mike zuwa masalaci dake ciki asibiti.

Har akayi isha'i, Essha Bata farka ba, mummy na makale a gefeta , wata likita daban tazo takara dubata ta tabatar musu cewa suyi na bada jimawa ba zata farka.Dare ya tsala dukasu ba bu Wanda ya runtsa mummy da Daddy,  hajiya da daddy k tun baya isha'i, Bala driver ya wuce dasu gida dun su huta.. Essha kuwa can tsarka dare ta farka batama gane kosu wa ye akanta sai kuka take tana fisge fisge tana magaganu" hajiya kuce mishi ya sakeni wlh basan aure, na tsaneshi, mugu ne, hajiya ki taimakeni"

Daddy da gudu yaje yakira likita dake da duty a daren yana zuwa ya mata allura bacci, mummy kam tayi kuka da Bata tabayishiba..

Washe gari sai misali 1:30pm na Rana Essha ta farka." Alhamdullila ta farka" maganar nurse din data zo dubanta ta ratsa dodo kunnuwansu haka yasasu juyowa a hautsune Dan gani zahiri abun da kunnuwasu suka jiye musu" Tabbas ta farka" mummy ta fada lokaci da idanuwansu suka hade waje daya, da sauri ta karasa wajenta tana " Essha daddy" ta fada Tana kokari ruko hannu ta, Essha ta Mike da ga kwance da sauri  ta rugume mummy ta, ta fashe da wani kuka Mai kashe jiki Mai sauraro, mummy ma haweye takeyi tana shafa kwantace gashi ta da ya gaji da hargitsewa.

"Mummy tsoro nakeji inaji fargaba mummy, su aurar da ni, they have ruined my life" ta Kara sauti kukata, daddy ya matso kusa da su ya shafa kanta, a firgice ta juya tana gani shine ta rugumeshi " Daddy zuciya, daddy kasana, zan mutu daddy, ka raba aura na wlh banso, shikena an aura dani daddy na bazai kaini makarataba balle na cika burina har yakai ga kirana DOCTOR ESSHA, nasan daga Rana ita yau zan daina sa .... Ta dakata, jiki ta har rawa yake saboda tsumayi kuka" daddy why me? Why? Why? 

Daddy haweye fuskata yashiga gogewa shima dauriya kawai yayi, Yana rike haweye bai barsu su sauka ba ya daure yayi murmushi Yana girgiza Kai yace" ya'isa haka Essha daddy, ki daina ai'bata aureki Kar ki mantafa aure sunnah ne na Ma'aiki (S.A.W), aure rahma ne Kuma alkharine, magana karatu inshallah ba abun da zai hanaki bearing suna DOCTOR ESSHA" yaja mata kumatu yayi murmushi " ba abunda zai saimeki inshallah, ni da mummy ki dasu hajiya muna tare da ke"
Daki ya dauki shiru, bakaji komai sai shesheka kuka Essha da hajiya,  Essha na kuka zafi da ke damunta, hajiya Kuma tausayi hali da Essha ke ciki shiyasa ta kuka, Essha sai zabura  take ita daya, haryanzu da alama tsoro a atare da ita, daddy nata aiki lallashi, can ya Mike yace" Essha zanje sallah ankira zuhur"

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now