Birthday party

164 10 0
                                    

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
DOCTOR ESSHA
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

WRITING BY
J Hajara

🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M.W.A*

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoya ta. 🤙🏻
https://www.facebook.com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

5️⃣6️⃣&5️⃣7️⃣

Pooja na parking ta fito, ta shiga ciki jiki a sanyaye, ciki gida ta tarar da yara da manya. An decorating gida da ballons gabadaya, ta nufi parlor, takara gani wani decorations da ya rudata
Ya yi kyau batasan sanda ta furta wow ba, gaskiya decoration din birthday din ya mata kyau, har wani babba balloon aka sa a sama tsakiyar parlor, tsakiyar parlor kuwa center table da yasha decorations me kyau aka Daura babba cake na favorite cartoon show na Sadik wato PJ Masks, wow cake din PJ masks ya hadu, Ash color ne jiki cake din, left side din kuwa owlette ne, middle Kuma cat boy , right Kuma gekko,( Don't mind me ooo😆 duka sunayana actors din PJ masks ne, Kar kurikece😁).

Tsakiyar cake din kuwa 7 ne Mai dauke da candle a ciki( Kai gaskiya Mai cake din ta kware) .
Pooja ta share hawaye tana ta shafa cake din a hankali tace" Sadik mummyka na matukar sonka, tana tsoro abunda zai rabaku ne kawai, but very soon nasa komai zai zo mata da sauki" ta Kara bin parlor da kallo decoration din ya gama haduwa, harda number Balloons Mai dauke da seven da aka kafashi a tsakiyar aluminum balloons dake gefe parlor, gefe guda Kuma Happy Birthday Sadik akasa da flowers na zangaye da rubutu, ga white bulbs da akasa a gida gabadaya sai ya bada wani yanayi Mai kyau da annashiwa, Kai guri birthday yagama haduwa, Pooja ta nemi guri ta zauna tana bin yara da ke ta wasa su da kallo, can Arundh ta shigo da guduta ta Sha wanka tayi kyau gashi kana yasha gyara, Pooja ta kirata tana tambayarta Ina su sadik? Ta Bata amsa da cewa taje Airport dauka brother dintaa"

Da Hindi tace" mummy surprise birthday ne fa aka hada ma sadik,Bai saniba, ama mummy guri ya mi kyau"

Pooja tayi murmushi tace" nasani saura kifada Mai da baki ki na surutu na"

Arudh ta rufe baki tana dariya...

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

Essha ne ke tuki a hankali harta iso Airports din, tana fitowa sai waige waige take tana neman Amir, can ta hangoshi zaune ya makala earpience a kunne, sai danne waya yake hankalishi a kwance, Batama ganeshi ba, sanda ta Kara murza Ido da kyau, Amir ya Kara girma yazama wani handsome guy, da sauri ta karasa wajashi ta bashi bugu Wasa a kafada tana murmushi. Amir naji a tabashi ya Mike a zabure, Yana ganita yafara zuba murmushi cike da tsokana yace" kaga manya ba, Doctor Essha, sis kiga yanda kikara kyau, wow sis bamarabaki da indiyawa ma"

Taja mishi kunne tana murmushi tace" haryanzu baka canza bako, da tsokanar na"

Yayi murmushi yace"sis Ina fa zan canza, gaskiya sis we really miss you, Daddy yace nafada Miki gobe, gobe na ba sai jibi ba, ki koma gida, kiga zamu koma tare kenan"

Essha daji haka jikita yayi sanyi, ba haka tasoba, ama dole tabin umarni Daddy, tafison ako yaushe ta riga farata mishi..

Amir ya katse mata zance zuci ta da " where is my son? Yau ne birthday shi ko?"

Tayi murmushi ta kada Kai ..

Yace" toh Ina yake?"

" Kai amir sauri Mai kake, yana gida nannyshi tana shiryashi,muje na daukoshi "

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now