Allah yabarmu tare

615 27 2
                                    

👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️
        *DOCTOR ESSHA*
👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️👩‍⚕️

*Written by J Hajara*

🌍 *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️✏️

          *M. W. A*

   '''Kungiyar d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoyan ta.
https://www. Facebook. Com/107980080946102? referrer=whatsa
___________________________

*Bismillahi Rahman* *Rahim 🙏*

   *ALHAMDULLILAH*
😌😁😌🤗😀😌😁😌
      *ALHAMDULLILAH*
🤭💃💃💃💃💃🤭

             1️⃣0️⃣0️⃣

*Lusa'il Stadium Qa__tar*

Cike Stadium din yake makil da Mutani daga kasashe Duniya Baki daya, jinsi Al'adu kala kala, Sai dai shigarsu ce dai ya so yayi kala daya, dake garin Larabawa ne Kuma kasar musuluci, Dayawa Mata na Sanye ne da Abaya,Maza Kuma Jalabiya ne  Farare kal kal a jikisu,kansu Sanye da Ghutra ko keffiya, irin shiga da maza Arab keyi (shiga irin na Larabawa)  Wasu su kuma na Sanye ne da Jersey Na kasashe  biyu da za abuga Wasa Karshe dasu wato kasar France da Argentina.

Can sama wajen zama Yan Vip na hango su Essha Mashallah ta hadu, baza ka ma gane ita bace dun ta canza ta murje sosai takara wani kyau Kamar wata balarabiya(ah lalai Aliyu ya iya kiwo cikin sati daya har ya canza Mana Doc.Essha mu😅🤭) Sanye take da Abaya baka Mai balain kyau Sai walkiya yake, Aliyu na gefenta Ya subhanallah Shima kasa ganeshi nayi( sanda na Kara gyara 🥽 goggles Dina na matso da kyau) Uwa uba su Haidar dukanisu ba karami kyau sukayi ba, Kuma duk Tare da Matasu suke..

Bodyguards kuwa na kowani gefen ana tsaro lafiyarsu(kaji Manyaba)

"Allah banaso Argentina suci kofi Nan ko dun Saboda Messi" Suleiman ya Fada Yana Kara gyara zama  domin kallon Wasa da ake bugawa a tsakiyar filin dakyau

"Allah Nima, banason Yasamun WorldCup, yanda aka fitar dasu Ronaldo na tabata haka za'a musu dun Mbappe a shirye yake yau dina, Messi yaje gida ya kwanta suci zamanisu su bar ma Yara kuma" Hafiz ya Fada Yana sipping coke Dake Hannu sa

Kamiii(Matar Suleiman) tace"Baby nifa Argentina nake rooting dun Messi nakeso yaci kofin na"

Salma(Matar Haidar) tace" Ni ma su nake supporting, and I want to snap picture with him" tafada cikin shauki tana rike da kumatu

Haidar zare idonshi yayi yace" Da wa?"

Rage murya tayi Tace" Da Messi ma"

"Wlh kuwa Dana sa ma Stadium Dina wuta, kallonshi ma dakikeyi yanzu na kona min Rai, Allah yasa ma acisu 10-0" 

Duk suka fashe da dariya

Besty tace" zaku Sha Mamaki dun fa Kamar Messi yaci kofin na yagama"

Suleiman zaiyi magana Fawaz ya tareshi" Buddy yi shiru ka kallesu, kasan  ai su Dangi Messi ne(😅) Kana gardama dasu yanzu Sai cibi yazama kari"

Hafiz yayi dariya yace" ashe ka gane ai 0_0 ake zasu gani"

"Bari dai kaji...Ba garin gardama bane aka jefo ni nan, Kallon kwallo da banyi niyya ba da Ina na can a office Ina treating Patient" Fawaz ya Fada a hankali

Dariya suka soma mishi, Besty Kam harara ta jefamishi tace" Patient sufini kenan??"

"Da Allah kiyi hakuri ba ceba" 
Bai Gama rufe bakiba yaji Commentator yace
" It's a Goall for Argentina"  na kowa yatashi da Murna hardasu Besty

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now