Hadin Allah

193 6 0
                                    

Doctor Essha
👩‍⚕️
Written by J Hajara

2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣

Da sauri Essha ta Mike ta  nufi guri hajiya, Reza zai harba kenan tayi sauri ta buge  mishi hannu ya harbi iska tace

" ya fada wlh ya fada"ta rugume hajiya, hajiya sai ajiya zuciya takeyi kamar tayi gudu..

Aliyu sai binta da kallo yakeyi Yana murmushi Yana shafa kirji , Yanana sunata yafi a kirga sanan yace" Alhamdullila , today I have sight my lost rib, love of my life my preety , Abu fariciki ma a matsayi matata , Kai na Amince da aure na dari bisa dari " sai murmushi yake kamar gona auduga ...     

Oga yakalli shi yayi kwafa yace" toh fa za ' a daura aure "

Essha na jiki hajiya  sai kuka , hawaye wani na bi wani tace" shikena khalid  kayi hakuri basan da wani Ido zan kale ka bann. bansan... "

Hajiya ta katseta  tace" kiyi hakuri Aishatu , duk abunda yasamu  bawa haka Allah ya rubutamishi tun yana ciki.."ta goge kwalla ta cigaba " yau Yana daga ciki ranaku da baza taba mantawa dashi ba a duniya , ki ceci rayuwa ta Aisha , basan Mai zagayama ma Abba ki ...."

tana kan magana sukaji baba driver nacewa" An daura aure ALIYU UMAR DA AISHA AHMAD akan sadaki dubu dari fatihaaa"( Kai mutanina sucika shuumamu wato ma baba driver suka sa a matsayi Mai shela) ..

Essha naji hk ta fashe da sabon kuka , wani tuki baki ciki takeji  tace" hajiya ban sonshi , ban sanshiba , ki taimakeni ... "

Daddy k yazo ya dagata yace" Essha hkr zakiyi , haka Allah ya rubuta , addu'a kawai zamuyi yanzu mu fita na guri lafiya "

Daddy k yasami shugaban yace" toh shikena tunda an daura,ai zamu iya tafiya ko? ku sai kemu hakana.... "

Ai sai duka su ka fashe da dariya suna nunashi da bindiga , daya daga cikisu ya Mike zai tura daddy k.. Aliyu da sauri ya Mike ya kareshi Rai a bace yace" enough is enough, kun ce Kuna aiki Allah toh karyaku, Wana wulakatan bayi Allah kukeyi  Wanda Basu ji Basu gani ba , Kuna tauye musu hakkisu".

Daddy k ya dafashi yace" yaro kyalesu , akwai Allah , fada min Kai Dan inane , Ina son nasan asalika tunda ka auri yanta yanda shari'a musuluci ya tanadar?"

Aliyu zaiyi magana oga ya katsesu yace" Alhaji zai dai kuyi hakuri inkufita gari , zai ku tatauna ama ba yanzu , yanzu lokaci tarewa Amare ne, ga daki Amare na" ya nuna wanna bukka..  Daddy k da Aliyu suka binshi da kallo mamaki .. daddy k yace"  tarewa Kuma??"

Yace" Iyye tabbas , Essha zonan ..."

ya kwala ma Essha Kira kamar shi yasa mata suna..  Essha ta taho tana hawaye ta rakube a baya daddy k .. Aliyu na kallota Yana ji kamar ya janyo ta ya lalasheta saboda kuka na hurting feelings nashi sosai ..

Daddy karami ya fusata yace" bazai yuba, ku auran min da Yan na dole  , sanan kusasu su tare, inaaa Wana bamai yuwa bane"

"Kai yara ku daura min wanan sanan kusa mishi salatep a baki" oga ya fada a fusace...

  Hajiya ta karaso da sauri tace" kuyi hakuri yallabai ku sake shi , duk abunda ka shimfida muna zamu bi, ai ariga da an daura ba matsala " 

Oga yace" yawwa tsohuwa Ashe ki gane"

Daddy k ya marairace murya abun tausayi yace" haba hajiya..."

Hajiya ta daga mishi hannu tace" yi shiru banason na Kara ji murya ka ana umarni nake baka"

Aliyu ya daga Kai ya kalleta baice uffan ba Yana takaici Wana Abu..

Hajiya taja Essha ta rugumeta tace" Aisha Allah ya Miki albarka ..

DOCTOR EESHA👩‍⚕️Where stories live. Discover now