Babi na uku

12.6K 880 48
                                    

*inna ma'al usri yusrah,fa inna ma'al usri yusrah*

    Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali tare da jaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin 'yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata ita ma ta samu nata rabon,ta dora da cewa
"Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu da ke,haka kema baki damu kanki ba,ci da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani" maganar sai ta bama sumayya dariya da kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.

       Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan tace
"Ya mukhtar"
"Ya akayi sumy?" Ya fadi yana saurarenta.

    Sai data jawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ya dubeshi,cikin nutsuwar nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani
"Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta ba",cikin rashin fahimta ya tambayeta
" da akayi me fa?"ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace
"A ganina bai kamata ka dinga sa'insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutar da kai ba,a ganina auren nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa'iza ta haihu sai an fara cewa danka kafin a ce dan yaya yahanasu ko?" Ta dan sarara da maganar tana hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta.

     Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska
"Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?".

       Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa kawai take
" na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba'a yi mata lefe ba?bayan haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk wanda yaga laifina ko ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin"sai ta tashi daga saman kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kaana ta fashe da kuka.

     Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yana jin bata can can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki daya zuwa jikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin
"Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min" sai da taja hanci kadan sannan tace
"Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata"
"Shikenan an gama,sunci darajarki" sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace
"Na gode".

       Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta
" Allah yayi miki albarka"ya fada yana sakinta
"Amin ya mukhtar" ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa ko  yardarsa na tare da ta ubangiji.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now