Babi na talatin da takwas

9.5K 855 112
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ASSALAMU ALAIKUM*

*mas’alar saki uku cikin kalma guda*

idan mutum ya saki matarsa saki uku karkashin kalma daya ana daukan haka a matsayin saki daya ne tun asali.Haka wannan mas’alar take tun zamanin manzo S.A.W. har zamanin mulkin sayyadina Abubakar.A  Umar ya hau karagar khalifanci da shekaru biyu,sai sake-saken mata ya yawaita, don haka sai ya tsawatar da cewa; duk wanda ya sake sakin iyalinsa saki uku, to zamu dauka saki ukunne da gaske !!!

_A mazhabarmu ta Malikiyya wadda da ita muke aiki duk macen da aka saka saki uku a kalma guda ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da haka ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na_ _zamanin Umar RA, kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan_
_Allah ne mafi sani._
_Mafiya yawancin malamai sun rinjayar da saki uku a kalma daya ya tabbata saki ukun ne saboda toshe qofar barna kamar yadda sayyadina umar R.A yayi,saboda a zamanin da muke ciki muna hukunci da saki ukun idan akayi ya tabbata ya muka cika balle kuma ace ukun a matsayin daya yake?_
_Allah shine mafi sani._

***************************

*hhh,har yau fans kun kasa cankar dai dai game da abinda zai faru gaba cikin littafin kundin qaddara ta,saidai wasu kan kwatanta,so saboda haka ku bani gari kawai kuyi kurum kuci gaba da bibiya ta*
_______________________________

      "Lukman na da matar aure daya da yara hudu,hakan shike nuna zaiyi riqon Allah tunda har yana da wata matar ya saba riqon macen aure,bawai zaiyi aurensa na fari bane,amma kije kiyi tunani kina da sauran lokaci har kwanaki talatin,Allah ya zaba mana abinda yafi alheri,tashi kije".

       Tamkar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka take tafiya har ta isa dakin ta,kusan ranar baki daya akwance ta yita,tana jin abdallah yana qiriniyarsa har ya gama yayi bacci anan wurin.

  ****    *****   *****   *****

      Mukhtar bai fasa zuwa ganin yaronsa ba kamar yadda abdur rahman bai fasa zuwa gidan ba,saidai baki dayansu ganinta ya musu wahala,ba wanda take yarda ya ganta saidai bacin rana,ta bangare daya lukman naci gaba da nacin sake zuwa wajenta,saidai ko sau daya taqi yarda ya kuma zuwa din,wani irin so lukmam din ke mata wanda ke bata mamaki kuma ya fara sanya mata tausayinshi,duk randa baiji muryarta ba yakan zamo kamar wani soko ko zautacce,yayi ta jera kiran kenan har sai ta gaji ta daga,hakan ya sanya sau tari takan dan sassauta masa.

        Lokaci ne yaci gaba da tafiya,kwanakin da malam ya diba mata na kuma tafiya,a haka har aka cimma kwanaki talatin din cif,saidai shirun da taji malam din bai tada mata maganar ba ya sanya ta kwantar da hankali ta ta kuma sake sakankancewa abinta,har aka fara sabgar shirye shiryen auren yaya abubakar da ita.

   
         Ranar wata juma'a da wani yammaci wanda ya tasamma kwanaki arba'in da yin maganarta da malam bayan sakkowa sallar juma'a malam din ya dawo gida yaci abinci sannan ya sanya aka kira masa ita.

      Tunda taji kiransa hankalinta yayi mummunan tashi,a lokacin suna dakin mama suna shirya akwatin kayan lefan yaya abubakar da ake saka ran kaiwa satin sama.

      "Ya ake ciki sumayya,kwanakin da na diba miki sun shude har da doriya ba tare da naji komai daga bakinki ba".
Cikin yanayi na daburcewa tace
" eh malam dama.....dama.."
"Unhmmm,dama mene?,kin haqura kin zabi abdur rahman dinne" da sauri ta girgiza kai
"Ok,lukman din ne?" Nan ma kai ta girgiza,sai malam din ya sauya fuska sosai sannan yace
"Ki bude baki kimin magana sosai,idan ba haka ba zan bawa abdur rahman dama ya turo,saboda daga shi har lukman din babu mai aibu a cikinsa,aure kuwa mutunci da kamala shine abu mafi muhimmanci da za'a fara nema a cikinsa" tuni hawaye ya fara wanke mata fuska
"Malam bana son sake hada zama da su abdur rahman ka yimin afuwa" karo na farko da ta fara yima malam din musu,duk sai tajita wani iri,tana jin kamar tayi ba dai dai ba
"Shikenan,a bawa lukman din dama ya fito kenan?" Shiru tayi kamar wadda ruwa ya cinye,ta yaya zata sake musa masa bayan ba al'adarta bace?,baya ga haka kuma yayi bincike halayyarsa ta yi masa me zata ce kuma?,ganin batayi magana ba ya sanya ya sake maimaita tambayar tasa saidai nan ma shiru ne ya biyo baya bata ce komai ba,a bisa ga abinda addini ya nuna shiru alamar amincewa ce da hakan malam ya dauka cewa ta amince
"Shikenan,Allah ya tabbatar da alkhairi,Allah yayi miki albarka ya albarkaci aurenku,tashi ki tafi" abinda taji malam din ya fada kenan.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now