Babi na arba'in da bakwai

9.1K 854 100
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

_______________________________

     Bayan sallar isha'i ne,idarwarta kenan abdallah ya soma rigima tilas ta kwantar da shi gefanta ta soma lallabashi,don kwanakin abinda ya koya kenan rigima idan zaiyi bacci,ya Abbakar ne dake shirin wucewa gidansa ya leqo
"Kinyi baqo sumayya"
"Baqo?,baqo kuma ya abbakar?" Ta tambaya cikin mamaki da faduwar gaba,waye yake son jawo mata jarfa tana zamanta lafiyar Allah
"Eh baqo,kiyi ki fito kada ki zauna" ya fada cikin halin ko in kula da yanayinta yana sakin labulen ya fice,magabar tayita juyawa cikin ranta,sai ta banzatar da zancan jin yaya abbakar din na yiwa mama sai da safe ya wuce gidansa.

     Minti kusan goma da fitar tasa mama ta dago labulen ta shigo
"Wai ba yayanki ya fada miki kina da baqo ba" kamar zata saki kuka ta dubeta
"Mama ban fa san ko waye ba"
"Idan kinje kya ga ko waye din yana sitting room din malam,tashi maza ki wuce kuma  saura kije ki yiwa mutane sakarci",tilas ta miqe bayan ta kwantar da abdallah a kan gado ko hijabin jikinta bata cire ba ta fito zuciyarta fal quna.

       Turus tayi bakin qofar ragowar sallamarta ta koma ciki,da hanzari ta juya tana mai neman fita,cikin zafin nama ya sha gabanta wanda saura kadan jikinsu ya hadu,sai ta ja baya tana dubansa,mukhtar ne sanye da dinkim shadda ruwan sararin samaniya babu hula kansa,ta masa kyau sosai saidai ramar da yayi ta bayyana,hancinta ya cika da qamshin turarensa ya dinga tuna mata baya,saboda haka da sauri tace
" matsamin na wuce"
"Babu inda zakije sumayya yau sai kince wani abu game da ni,kin yafe min ko baki yafemin ba,sumayya ya ina kike so na dora raina?,laifi ne na aikatashi na nemi afuwarki sumayya amma kinqi kice komai,kinsan kullum ya nake kwana ya nake tashi da rashin cewa komanki?,kinsan me nakeji cikin qirji na" sai kuma ya sassauta murya cikin sanyi
"Kinfi kowa sanin wane mukhtar sumayya,kinfi kowa sanin wane irin zama mukayi a baya,sumayya ki tausaya min koda ba zaki tausayamin ba ki tausayawa abdallah,abdallah ya zama marayan qarfi da yaji,abdallah na buqatar mu ni da ke a tare,idan baki tausayawa mana ba sumayya waye zaiji tausayinmu duk duniya?,taba qirjina sumayya kiji" ya fada yana fincikar hannunta zuwa qirjinsa,sosai taji zuciyarsa na bugawa,gaza cire hannunta tayi sai da taji ya ambaci wash,da sauri ta dubeshi sai taga yana dafe da kansa yana layi,batasan sanda ta riqeshi ba a rude tana cewa lafiya?,ganin yana neman gun zama ya sanya ta zaunar da shi tana masa sannu,tsahon mintina biyar sannan ya sauke numfashi ya gyara zamansa tana zaune can nesa da shi ya dubeta
"Ciwon kai nake fama da shi,amma wannan duka ba damuwata bace burina kawai ki yafemin" ya fada yana duban qwayar idanunta,a hankali ta janye idanuwanta zuciyarta na mata bitar waye mukhtar agurinta,
"Na yafe maka" ta furta murya can qasa
"Allah ya yafe mana baki daya" wani wawar ajiyar zuciya ya saki,baki daya jikinsa ya saki,wani farinciki yaji yana ratsa kowacce gaba ta jikinsa,yana so yaje ga sumayyan amma sam jikinsa babu qwari ko kadan,sai ya miqa mata hannu
"Taso sumayya kizo kusa da ni don Allah" sai ta girgiza kai ba tare data motsa ba,tilas ya tattaro duk wani ragowar qarfinsa ya kiqe ya isa gareta,kusa da ita ya zauna har tana gogar kafadarta,hakan ne ya sanyata ta janye da sauri tana hada rai
"Meye haka,don nace na yafe maka ai hakan ba yana nufin kai mijina bane ko zan sakw aurenka ba" da sauri ya sake matsawa kusa da ita babu gun matsawa a gunta don ya kaita qarshen kujerar sai ya kama hannunta ya matse cikin nashi
"Sumayya,na sake miki wani laifin don na bada sadakinki,amma bisa sharadin matsawar baki amince ba zan karbi kaya na na haqura"
Wani abu taji yana ratsa zuciyarta mai kama da farinciki,zuciyarta ta karye hawaye ya biyo kuncinta,cikin raunanniyar murya ta kwabe fuskarta
"Ni nace maka ka kai sadakina ba tare da sani na ba?,ai kuwa sai kaje ka karbi abinka don ni ban amince ba,kuma......" Bata ankara ba ya hade bakinsu waje daya wanda hakan yayi sanadiyyar katsewar maganarta,sun dauki kusan minti goma a haka sannan ya janye yana dubanta,qasa tayi da kanta kan fuskarta qaramin murmushi na fita a fuskarta
"Magana ta qare,na sanki tun ba yau ba,dukkan abinda zaki fada a yanzun nasan aji ne kawai za'a jamin ko ba haka ba" sake hade fuska tayi kamar gaske
"Nidai na fada kaje ka karbi sadakinka,bana yi"
"Ok to bari na kira ya abbakar na sanar masa" ya fada yana fiddo wayarsa daga aljihun gaban rigarsa,ganin da gaske lambar ya abbakar yake nemowa ya sanyata qwace wayar
"A'ah,ki bani mana na isar mishi da saqonki"
"Ni bance ba" ta fada a shagwabe,sai yayi jagale yana kallonta saboda tuna masa da baya da tayi ta salon yanayin maganar da tayi
"Kada ki hanani fa tafiya gida yau na kwana a nan"
"Bismillah mana ai ga guri nan" sai yayi kalar tausayi yana dubanta
"Yaushe za'a tara shaidu sumayya ki koma dakinki" idanu ta juya ta dan murguda baki
"Sai shekara iwar haka" qirjinsa ya dafe yana kallonta
"Mutuwa kike so nayi kafin lokacin sannan ko?" Rai ta hade
"Ka daina fadin haka mana ya mukhtar,ni kunya nake ji gaskiya ka bari idan ja shirya zan fada maka ka sanarwa ya abbakar" hannunta wanda ke cikin nashi ya sumbata yana fadin
"Na gode,na gode,na gode sumayya,na gode da karamcin da kika nuna min a rayuwa,na gode da kika nuna ke mai qaunata ce har yanzu" sai ya dakata yana fidda zoben azurfan dake yatsansa ya zura a nata,ya mata yawa hakan ya basu dariya baki dayansu,sai ya cire ya sanya mata a yatsan tsakiya duk da haka ya mata yawa
"Ina son zoben nan sumayy,amma sai naga yafi kyau a hannunki,ki ajiyemin zan karba"
"Idan kuma naji dadinsa bazan maida maka ba"
Dariya ya danyi sannan yace
"Babu komai,ai da kai da kaya duka mallakar wuya ne" sallamar halima ta sanya sumayya miqewa,shigowa tayi dauke da abdallah tana fadin
"Wallahi yaron nan ya koyi rigima,tunda ya tashi yaje zunduma ihu nayi tsammani ma kin jiyo shi"
"Ina zata jiyoshi ta shiga kogin qauna" mukhtar ya fada cikin salon zolaya yana miqa hannu ya amshi abdallah dake ta dokin zuwa gunsa yana kiran abba na,murmushi halima tayi tana yiwa sumayya kallon tsokana ta fice,ita kanta wani dadi taji don babu wanda yaji dadin rabuwarta da mukhtar,qafarta har qaiqayi take taje ta bawa zainab labari.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now