Babi na sittin da tara

12.1K 1.1K 145
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

ALLAH S W T YANA CEWA

*YAKU WADANDA KUKA YI IMANI KU CIKA ALQAWARURRUKA

_______________________________________


         Sosai wannan karon zaman kano yayi mata dadi,har vata so ta tuna zata koma abuja,tayi ziyara gidajen 'yan uwan mamanta,kowa yaji dadin ganinta.

        Ranar bude asibitin abdur rahman kuwa baki daya 'yan gidan sunje,maama kawai suka bari a gida,sosai asibitin yayi kyau,duk da yake ba wani girma gareshi ba,kamar wajen bada magani ne amma na islama wato islamic medicine center,amma akwai dakuna guda goma masu dauke da gadaje saboda halin lalura da za'a iya kawo mutum ciki,yaso sumayyan ta tsaya su wuce gida sabida akwai walima daga nan sai ya dawo da su amma taqi saboda yana cikin jama'a masu tayashi murna bai kammala sallamarsu ba,bugu da qari tana kunyar hajiya kada suje tare yayi wani abu da zai fallasa su,a gurguje taje ta yima hajiya da kawu murna suka koma gida.

       Ko da yazo ya taras ta tafi sai da ya kirata yayi mata qorafi,dariya kawai tayi ta bashi uziri,yace ya haqura amma da sharadin zata rakashi randa zai fara zama office dinsa,binshi tayi da to don samun mafita ba don zata din ba.

        Sosai ta miqe qafa abunta,gida yayi mata dadi,wani lokaci tana gida wani lokaci tana gidan ya abubakar amina ke dauke ta,a irin hakan wani weekend abubakar din ya zauna gida bai fita,lissafi ya zauna ya yiwa sumayya na kudadensu,ita kanta tayi mamakin yadda kudin keta ci gaba yana habaka,kada ma na Abdallah yaji labari,tasan hakan kuwa baya rasa nasaba da kyakkyawan ruqo da abubakar ya yiwa dukiyar tasu
"Na gode yaya abubakar,Allah ya qara zumunci ya raya maka zuriyarka"
"Haba sumayya,ai dukiyar maraya da mutane sunsan bala'in dake ciki da basu taba ta ba,ko kin manta cewa Allah S W T yake cewa 'haqiqa wadanda suke cin dukiyar maraya da zalunci(barna da mugunta)haqiqa suna cin wuta ne a cikinsu,da sannu zasu shiga wutar sa'ira,duk mai hankali babu abinda zai kaishi afkawa wanann babbaf musibar,bare ke da kike 'yar uwata,idan banyi miki ba wa zan yiwa" kai take gyadawa cike da gamsuwa
"Gaskiya ne,Allah ya sa mu dace"
"Amin" ya fada yana qwalawa amina kira wadda tunda taga zasuyi magana ta basu guri,babu yadda sumayyan batayi ta zauna ba taqi.

       Cikin kudaden da sukayi lissafi an fidda riba mai yawan gaske wadda take ta shekara daya,ta raba ta kashi biyar,daya ta baiwa mama,daya ta baiwa malam,daya ta ajjiye a hannunta zata yiwa zainab siyayyan kayan kallo,plasma t.v,d.v.d,home thierther don sauran daidaikun kayan kitchen,don su kadai suka rage,tuni ya abubakar ya kammala siyan komai,daya kuma ta baiwa ya abubakar,zata kashewa abdallah sauran kason duk da babu abinda ya rasa,qememe suka qi amsa baki dayansu suka maida mata kudin,don su a ganinsu itace abar atallafa maga,sai data yiwa malam qwalla tace albarka take nema sannan ya amshi na gunsa yace zai bawa maman nata a ciki,ya abubakar ma biyu ya raba ya dauki rabi suka dawo mata da saura,itakam bata san me zata yi da su ba sukaje uta bata da buqata,itama ta kashe,murmushi tayi donbita kam bata da matsalar komai,sutura harda sababbi wadanda bata taba sanyawa ba tana da su,abinci da abunsha ma sai wanda ta zaba,ya abbakar ta fadawa yace zai bude mata accnt kafin ta tafi ta karbi atm din,hakan yayi mata ta sake yi masa godiya,babu abinda zata ce da Allah sai godiya,ya bata iyaye da 'yan uwa masu sonta.

        Wani abu ta cira cikin kudin ta baiwa ya abbakar taje waya take so guda biyu,kwana biyu tsakani kuwa sai gashi da manyan wayoyi masu bala'in kyau,saidai sun danci kudi,ta bare dayar ta jona a caji ta barwa mama ta hannunta,ba wani jimawa tayi ba uncle farouq ne ya sauya mata ita kafin su tafi,dayar kuma ta ajjiye da niyyar ta kaiwa anty dije tsarabar kano.

          Satin ta biyu a kano amira ta soma matsanta mata da waya,murmushi tayi
"Ina nan tafe nan da wani satin,ina cewa saura sati biyu dai ko?"
"Zamuje gombe,zanyi sati daya,gaskiya ki tabbatar sister kin dawo din cikin satin nan,Allah baki daya plan dina ya rushe,nafison naga komai kina kusa,komai ni baya min yadda nakeso,nasan da kina kusa abin sai yafi haka,kinga rashin zuwanki dubai wlh har kusan fada mukayi da anty su'ad,baki ga tarkacen da taso hadomin ba kawai abu idan ya burgeta a ido ko bata san amfaninsa ba sai tace a dauko,sai da na botsare mata nace bana so,harda hadani da ya man yace ta barni ja zabi abinda nakeso,tunda na fita sanin muhimmancin kayan kitchen" sosai ta bawa sumayya dariya,idan tana wani abun kamar qaramar yarinya
"Shikenan,zanyi qoqari na dawo insha Allah,gida ne akwai dadi wallahi"
"Na sani,amma pls sister kiyi qoqari don Allah"
"Insha Allah" da haka suka rabu

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now