Babi na ashirin da tara

8.2K 674 32
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*kullu man alaiha faan,wa yabqa wajhu rabbuka zuljalalu wal ikram*

_dukkan wani abu dake kanta(duniya)qararre ne,zatin ubangijinka mai girma da daukaka ne zai dawwama_

*Na sadaukar da wannan page da dukkan wani makarancin littafin KUNDIN QADDARATA,haqiqa zan so ace ina da lokaci da zan iya binku daya bayan daya na amsa commenta naku,saidai ina fatan wannan shafi ya isar muku,na gode qwarai*

_masu qorafe qorafe kuyi haquri,ku karbi littafin a duk yadda yazo muku,da fatan kunyi duba da ayar da tazo a farkon shafin,ita kadai ta isa ku fahimci me nake nufi,godiya nake_

Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga kwanciya sai bacci,ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta,duk lokacin da ta yunqura ta yiwa kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa ko kadan bata da sha'awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,banda ruwa babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya jefo mata wanda zaya taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka ta shafe kwana hudu cur bata ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa taci ranar girkinta har ta fita amma bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama ta riga data saba da hakan,data ga irin hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa zainab.

**** ***** *****

Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji sauqi sauqin jikinta,tana jin qwari qwari a jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi wanka,tana fitowa ta soma laluben wayarta,can cikin jakar da ta dawo daga gidan anty dije ta ganta,a nan taci karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji dadin kudin don bata da ko siai a hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba sana'a take ba,caji ta sanya a socket din dake daura da madubinta,ta dawo bakin gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda take zaunen tana iya hango kanta sosai cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da ita,sai uban fari da ta qara kamar wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.

Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi bakin qofar,mukhtar ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya ciza,yayi kyau sosai amma sai taga kamar ya rame,duj da bata sani ba ko idanunta ne,don idan ba makuwa tayi ba rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a qirjinta.

Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa amma ya rasa duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa wadda ya azata a bigiren tausayi,uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda bai jin soyayyarta cikin zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa manta,ta bude drower dinta ta fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma dubansa
"Ka fita don Allah zan sanya kaya" ta fada idanunta tsakar nashi
"Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa ranki ne kamar yadda zainab ta fada?"ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na farko ba
"Kan bala'i" ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan rainin hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta?
"Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki" ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa inda take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta kwanakin bakwai din nan da bai ziyarceta ba
"Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama naki". Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.

" lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?"haka ya dinga fadi yana riqe da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now