Babi na casa'in

20.6K 1.4K 496
                                    

Bismillahir rahmanir rahim

YA UBANGIJI KADA KA JARRABEMU DA AZZALUMAN SHUGABANNI SABIDA ZUNUBANMU KAJI QANMU,YA ALLAH DUK MAI NEMAMMU KO NUFINMU DA SHARRI ALLAH KA MAIDA MASA DUK ABINDA YA YI TANADI A KAN KANSA YA KOMA MASA
____________________________________

Kai kawai ta kada ta juya ta fice daga dakin,bata so tayi wani abu da zai sanya almustapha yayi misbehaving dinta gaban sumayyar,don ta riga data sani ta bata masa rai qwarai,ta kaishi bango,hakanan fushinsa bai da kyau ko kadan,idanunsa ya dauke daga kanta bayan ta fice ya dubi sumayyan sanda ta gama,daga boxer sai singlet,da idanu ya nuna mata singlet din,a kunyace ta cire mishi,ya sake nuna mata boxer din,sai ta kauda kai tana turo baki,itakam ba zata iya ba,shi ko nauyin su'ad baiji ba zai wani ce ra cire masa kaya,zata juya kenan ya janyota jikinta,ya matseta cikin jikinshi yana goga fatar jikinsa jikin tata,tsigar jikinta ta zuba saboda yawan gargasar dake jikinsa
"Ina zaki baki gama ba?"
"Na gama mana,na bar baquwa ne a qasa"
"Idan ina nan kisa a ranki babu wani a gidan nan sai ni da ke,abidan ce baquwa?,ki tambayeta haka takewa hamza?" Shuru tayi murmushu na qwace mata,sakinta yayi ya nufi bandaki yana cewa
"Kayan nan akwai zafi,but akwai dadi da kyau kayan al'ada" kanta ta maida inda ya yasar da babbar rigar,kana kallonta kasan bata jima jikinsa ba,hakan yake ko a can din ma cireta yayi ya riqe a hannunshi,gefan gadon ta koma ta zauna,wayarshi ta soma ruri,musaddiq ke kira,ganin haka ya sanya ta daga ta shaida musu wanka yake
"Au shine ya zube mu a wannan da yake shine agwagwa sarkin wanka?,tell him muna jiranshi" murmushi kawai tayi ta datse kiran,abotarsu na burgeta,kawai sun dauki kansu daya ne baku daya su shidan,qaraso yayi ya miqa mata hannu sai ta dora wayan saman tafin hannunsa,ya fara shafawa yana tambayarta waye ta sanar masa,sai ya dan tsuke fuska
"Why you permit him yaji muryanki?"
"Afuwan" ta fada a sanyaye,sai ya dan saki fuska yana ajjiye wayar tare da takowa inda take zaune,gab da ita ya zauna har suna gugan juna
"Ina da kishi,matsanancin kishim da bansan ina da shi ba sai da muka kasance tare,please ki kiyaye"
"In sha Allah", mai ta dauko ta soma shafa masa bayan ta gama tsane masa jiki,duk inda ta zagaya ko ta gifta qamshinta na bibiye da ita tare da cika masa hanci,cikin wani cotton yadi fari qal mai adon ash ya shirya,ba qaramin kyau kayan suka masa ba,sai ta dinga satar kallonshi ba tare data sani ba,shigar na qawatar da ita,jikin bango ya rutsata tsaye,tana shirin yin qasa da kanta ya riqe fuskan
"gulma.....kema kin iya,me yasa ba zaki bude baki ki magana ba?" Murmushi ta saki,sai ta saka idanunta sosai cikin nashi ta juyasu tamkar mai yin faari,hakan ya rudashi,ya sanya tattausan lebbansa ya sumbaci idanun nata,qarar wayarshi ta katse masa abinda yake shirin yi,ummee ke kira,ta sanar masa baba na son ganin sumayya a falonshi,ya sauke wayar yana dubanta
"Baba ne ke kiranki,but bana so ki fita,a cike wajen yake,muje na rakaki"
"To" ta amsa ta juya da niyyar ficewa,har ta sanya qafarta waje yace
"Hey" juyowa tayi tana dubanshi,da hannu yake kwatanta mata
"Ina hijabinkin nan babba wanda ya sauko qasa?"kai ta gyada
" yauwa,shi zaki sanya"
"To" ta amsa tana ficewa,wayarshi ya ciro ya kira su lamin ya shaida musu yana zuwa zaije wajen baba ne ya dawo,a dakin ta tadda abida har ta soma gyangyadi abinta,tace tana zuwa
"Babu komai,gama uzurinki,ni wannan kwanciyar ta fimin komai dadi" murmushi tayi ta fice tana tausayin abidan,tayi nauyi qwarai,duka duka watanni kadan suka rage mata ta haihu,ba lallai ma tabi hamza a gida taje tunanin zama har sai ta haihu din.

Tana gaba yana biye da ita kamar wani body guard,hakan ma yayi masa,tunda ko banza yana morewa kallonta,kasa control din kanta tayi sa'ar da taga malam da abdallah,da gudu yaron ya nufota ta duqa ta tarbeshi ya fada jikinta ta rungumeshi
"Ammi......ashe nan kika dawo kin bar gidan umman khalipha.....laaaaaa,daddy?" Ya katse maganar tasa ya dora da wannan sanda suka hada idanu da almustapha wanda ke tsaye hannayenshi harde a qirji,sosai abun ya masa,sai ya tuna sanda ya ganta da hijab cikin ranakun bikin amira,ta bude hannunta kamar haka yaran suka shige,kwadayin samun yaranshi ya taso masa ya kuma sake nunkuwa fiye da da,don a wannan lokacin haka kawai yaji yafison yara fiye da baya,yana jin dama ace abdallan nasa ne,yaron ya shiga zuciyarshi,amma tana nufin itace mamarshi?,Allah ne ya kiyaye bai kai mata bugu ba randa ta bugeshi kenan,sam bai sani ba,barin jikin sumayya yayi ya nufo almustapha,cak ya dagashi sama murmushi na subucewa daga fuskanshi,sama ya dinga juyashi abdallahn na dariya,yana son ayi masa hakan dalilin da yasa ya kasa manta almustapha kenan,dauke kanta tayi wani farinciki na ratsata ta isa gabansu baba ta duqa,cikin qauna ladabi da girmamawa take gaidasu,cikin kukawa baki daya suke amsawa kafin baba ya dora
"Haduwa tayi wuya mamana,tunda kuka dawo ban ganku ba" kai ta sadda qasa tan murmushi
"Ummee tace kaje jigawa ai sanda muka iso"
"Gaskiya ne kam,ina fatan komai lafiya?,ko da yake alamu sun nuna hakan,saidai muci gaba da binku da addu'a" murmushi taci gaba da yi ba tare data tanka ba,dai dai sanda almustapha ya qaraso ya durqusa gabansun kamar yadda sumayya tayi ya soma gaidasu suna amsawa,ta dan saci kallonshi sanda yake tambayar mama da yaya abubakar,baba ne yace a basu waje da sauri malam yace
"Haba muhtari,waye baqo cikinku,me zan gaya mata me zata gayan,ka daina min haka" dariya baba ya saki ya koma ya zauna,hira suka taba sama sama duk da sumayya ta kasa sakewa,daga bisani ta dauke abdallah ta basu waje,malam din ba sai ta kawo masa komai ba,idan ta aikata hakan ma kamar tayi rashin kunya kenan,don ita kanta ba zata iya qayyade yawan abincin dake gabanshi ba.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now