Babi na tara

10.5K 924 101
                                    

Bismillahir rahmanir rahim

*wa iy yamsaskallahu bi durrin fala khaashifa lahu illahuw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih*

        Ya rantse sai ya hukunta ta,sai ta gane bata da wayo,'yar bariki ce ita ko mai,zai nuna mata bata iya iskanci ba.

         Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa
"Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsuu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta
"Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin
"Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi.

         Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom.

          Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba
"Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.

          Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika.

          Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.

      Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da dakon fitowarta.

        Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya dawo ya sameta tsaf.

        Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan
"Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace
"Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace
" eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata
"Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.

         Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna
"Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now