Babi na biyar

10.1K 839 52
                                    

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_la yadillu rabbi wala yansa_*

_ina taya maman farida(dan maliki,baya tsami banza,hanyan ruwa)murna sauka lafiya tare sa samun zan kadeden baby boy,Allah ya raya mana shi cikin musulunci,ya albarkaceshi,ya qara musu lafiya ita da babyn,sannan kuma muna kamu tun yanzu,lol_

    Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayi jim yana jiran amsa sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar
"Da wa nake magana?",cikin karyar da murya akace
" mukhtar baka ganeni ba,fa'iza ce fa"
"Fa'iza?,wacce fa'iza" wani murmushi akayi mai fidda da sauti cikin siga ta nufin jan hankali
"Fa'iza amaryarka mana".

       Hade rai yayi kana cikin dakiya yace"ok,ya akayi?",sake marairaice murya tayi
"Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?"
"Yayi kyau,ina gajiya?"
"Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin sake zuwa guna bakayi,haba"
"Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?" Kai ta girgiza kamar tana gabansa,cikin ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa
"A'ah ba shi bane"
"Fadi uzirinki kai tsaye".

      Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana
"An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka bawa uwar gidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantar ciki da falo"tana direwa ya dora
"Ko?,a wanne hadisin?".

     Fara quluwa tayi amma ta dake"haka na ya dace ai"
"To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki haqqinki" ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don kada kwabarta tayi ruwa
"Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba" tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki.

      Itama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare.

      Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tana jiran dawowarta,ita ta gyare mata jikinta fes,zuwa la'asar ta fito shar,fatarta ta sake wani kyau da haske.

    Tsokanarta sosai mukhtar ya dinga yi,yana mata waqa
"Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)" dariyar itama ta dinga yi.

     Ranar juma'a aka zo aka mata lalle ja da baqi,ta aika halima da zainab suka karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya.

       Wuni tayi babu laifi ta dan tara jama'a,sosai mutanen unguwar suka yi mata kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata suna jira a kawo amarya su karbeta.

       Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya kada 'yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshe jikinta sannan ta nemi baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo.

       Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na darw babu ita babu alamarta,hakan ya sanya maqotam suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa 'yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za'a bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama suka tafi,maman nana kawai ta rage.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now