Babi na talatin da hudu

10.3K 974 117
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wallazi yumutuni summa yuhyi,wallazi adma'u ay yagfirali khadi aty yau maddin*

______________________________

       A makare ya tashi yau wanda hakan ya sabba ba masa yin sallar asubahi cikin gida,tunda ya idar da sallar yake zaune saman daddumar bai tashi ba kamar yadda bai aiwatar da komai ba,tunanin sumayya ne fal zuciyarsa yau ya wayi gari da shi,hakanan yake jin wunin yau ba zai iya qarewa ba ba tare da yaje ya ganta da lafiyar abinda ke cikinta ba,kusan tunda ta shiga watan haihuwarta da ita yaje kwana yake tashi.

       Qarar wayarsa ce ta katse masa hanzari,ya juya bangaren da take ya jawota ya duba,baquwar lamba ce,ya latsa sannan ya kara a kunnensa,runtse idanunsa yayi zuciyarsa ta soma quna saboda muryar wadda yaji,bai taba jin ya tsani wani abu tsana mai tsanani ba irin na mamallakiyar muryar,zainab ce take magana cikin maqale murya da wani irin salo nason tafiyar da hankali,tun a daren jiya bokanta wanda take kira da malam ya bata wannan sa'ar ya kuma tabbatar mata bayan sallar asubahi ne zata sameshi,sanda ya daga wayar zuciyarta sai ta cika da farincikin samun nasara,don dama ya sanar mata bayan sallar asubar a gobe bazai koma bacci ba,jin tana ta magana ya mata shiru ya sanya ta fashewa da wani makirin kuka
"Habaa my mukhtar,dama laifin wani kan iya shafar wani?,mene laifina ni a ciki?,duk iya yina nayi don inga abinda ke cikin yarinyar nan ya kubuta,duk tarin hidima dana dinga yi da ita rana daya duk ka mance ka watsar da alkhairi na a gareku ka sakeni,kuma ma tunda an samu cikin na nan ba shikenan ba komai ya wuce sai ka maidani daki na ko?".
Kamar garwashin wuta haka yaji kalaman nata,cikin harzuqa ya dakatar da ita
" ke wacce iriyar jahila ce wai?,shin kin manta zama ni dake a yanzu ya haramta ne sau nawa zan nana ta miki,ke koda kuwa ma zamanmu ya halatta bazan iya zama da kowacce mace ba a yanzu,tunda sumayya da na raina da kaina ta iya min haka babu wata diya mace da ba zata iya aikata min makamancin haka koma fiye da shi ba,saboda haka gargadina dake na qarshe,kada ki sake gigin kiran layi na ko tarar hanyar da kika san zan bi,idan kuma kinqi ji ba zaki qi gani ba"daga haka ya katse kiran ya ajjiye wayar a fusace.

        Daga daya bangaren nata itama ajjiye wayar tayi tana huci sannan ta dubi qawar tata
"Wannan wanne irin mutum ne haka?,duk zama da wuyar da muka sha wajen malam ta tashi kenan a banza,kinji maganganun banzan da yake gaya min?,to wallahi wannan karon babban aikin zan saka a masa koda duniya zata zageni,ko zanyi yawo babu zanin daurawa" kafada ta daga tana fadin
"Au ho sai yanzu kika gane kenan?,tuntuni ai malam din ya gaya miki ki saki naira kiga aikin da ko uwarsa dake kabari ba zai ganta a gabansa ba sai ke" miqewa tayi ta fice daga dakin fuuu tana fadin
"Ai anzo gurin kuma".

         A hasale ya kuma waiwayowa ga wayar tasa jin ta sake tsuwwa a karo na biyu yana zaton ita din ce ta sake kiransa,sai jikinsa yayi sanyi gabansa ya fara faduwa ganin sunan abubakar kan screen din,cikin sanyi da sallama ya amsa wayar,lumshe idanuwa yayi wata rahama na sauka cikin zuciyarsa lokacin da abubakar ke furta masa albishir mafi dadi da ya taba sauraro tsawon rayuwarsa,sumayya ta haihu ta haifa masa yaro,baisan adadin lokacin da ya dauka ba cikin duniyar madaukakin farinciki shidai ya farka yaga har kiran na abubakar ya katse.

       Faduwa yayi  saman a bin sallar yayi sujudush shukur yana mai tasbihi ga ubangiji,bai wani jinkiri ba ya miqe ya fada makewayi ya shiga wanka,cikin mintina talatin ya fito,kai tsaye gaban sif dinsa ya isa bayan ya tsane jikinsa,ya bude yana kallon kayan,a sanyaye ya sauke hannayensa yana duban kayan kala bakwai da suke sababbi dukkansu,ba zai manta randa ya bada dinkinsu ba,tun cikin sumayya na da wata uku a lokacin tana gidan,musamman ya tanadesu ya dinkasu saboda ya sanyasu tun daga rana ta farko da aka haifa masa yaronsa har ranar suna,baya iya manta lokacin da take dariya tana tsokanarsa da cewa gandoki,sai ya koma bakin gadon ya zauna yana yarfa hannu,yana jin yadda bacin rai ke taso masa yana son danne farincikin da yake ciki,baisan mai yasa har yau zuciyarsa ta kasa daina jin ciwon abinda tayi masa ba duk da cewa an cimma nasarar tsallakewar cikin gashi har yau Allah ya nufa ya iso duniya.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now