Babi na hamsin da uku

10K 856 67
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

_________________________________
*Allahu waliyyul lazina amanu yukrijahum minaz zulumati ilannur*

*haqiqa Allah shine majibancin lamarin wadanda sukayi imani yana fitar da su daga duhu izuwa haske*

GAISUWA MAI TARIN YAWA DA FATAN ALKHAIRI GAREKU 'YAN WATTPAD,BA SHAKKA INA JIM DADIN COMMENT DINKU,HAKA INA GODIYA DA ADDU'O'INKU.
_________________________________

        *GIDAN LUKMAN*

      Baki daya rayuwar gidan ta yiwa karima baqi,kusan ita kadai ke rayuwarta cikin gidan,yaran baki daya sun kwashe kayansu sunyi qaura zuwa bangaren hajiya,tsakaminta da su kallo daga nesa,suna dai shigowa su gaidata su kuma tambayeta mai zasuyi mata na aiki,hakanan duk abinda tace suyi matuqar bai sabawa addini ko al'ada ba hajiyan na umartarsu suyi mata,lukman kam tunda ya hada kayansa yayi tafiya zuwa legos tsawon watanni rabonsa da gida,saidai yakan kira wayar hajiya wanda ya siya ya ajjiye musu a bangaren hajiya,yana kira suyi hira da yaran ya kuma gaisa da hajiyan,sau tari idan tace ba zai dawo ba haquri yake bata,yace sam yaji gidan ya fice masa ne a rai tunda sumayya ta bar gidan,hakanan yana zama yana bata ran hajiyan,amma tayi haquri lokaci ne idan yayi zai dawo,sam karima bata san ya sauya lamba ba saidai idan ta kira tayi ta jin is switch off,hakanan a yanzu ba zata iya cewa ga inda lukman din yake ba,sai dai lokaci lokaci tana jin alert na transper din kudi daga account dinsa zuwa naga,kudin buqatunta na yau da kullum,sannu a hankali hankalinta ya fara tashi,wannan karon saboda rashin lukman din a kusa bata da isashshen kudi gunta da zata koma wajen malaminta.

   ********  *****  ********

    Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,kwanakin takabarta na raguwa,ta fawwalawa Allah lamarinta baki daya,hakanan ta karbi QADDARArta hannu bibbiyu,saidai ba'a raba zuciya da tuna abubuwa masu d'aci da suka gabatar mata,yanayin sumayya ya sauya baki daya,ta sake zama mai yawan shiru shiru,sai kallo da idanuwa,har yau jikinta ya kasa komawa dai dai,ta rame,sai uban fari data sake yi sanadiyyar ramar da tayi,anty dije ta koma sai ita a gidan da zainab da halima,su kawu sukace ta zauna tayi iddarta a dakinta don haka addinin musulunci yafi so,lokaci lokaci ya abbakar da matarsa da suke kira anty sukan leqosu.

     Ranar wata asabar wanda ya kama wata biyu da rasuwar mukhtar alhj farouq ya iso kano,cikin falon sumayya suke zaune kamar yadda suka saba idan zama irin wannan ya kamasu,bayan gaishe gaishe da qarin wani jajen alhj farouq ya soma gabatar da maganar data tarasu
"Bayan dukkan wani bincike da jami'an tsaro suka gabatar ya bayyana cewa zainab ita ta dauki nauyi ta kuma bada umarnin kisan mukhtar" duk sa suna zargin hakan amma sai da maganar ta sake razanasu,kuka yaya yahanasu ta sanya tana salati da kalmar shahada tare da ambatar sunan zainab,alhaj farouq bai kula ba ya dora
"Ta bayyana dalilinta na yin hakan da cewa bacin ran wulaqancin da mukhtar ya mata ne na saki uku kuma yaqi maidata bayan kaahe kudaden da tayi wajen bin malamai amma babu nasara,qarshe ma ya bita da dukan kawo wuqa,daga bisani kuma ta tsinci labarin ya maida aurensa da sumayya bayan ita ta kamu da cuta mai karya garkuwar jiki ta sanadinsa,tunda taga haka ta tabbatar bazai mayar da ita ba,sai taga gwara ayi biyu babu kowa ya rasa,baya ga haka dama tana jin haushin sumayya na tsallake rijiya da baya da tayi har ta haifi abdallah"alhj farouq ya saurara yana maida numfashi cike da bacin rai,ji yake kamar ya shaqe zainab a lokacin da take wannan bayanin,tun asali shi mutum ne mai tausayi da jin qai,baya qaunar zalunci sam a rayuwarsa
"La ilaha illa anta,yanzu sakayyar da zainab kika yi mana kenan,ashe kece ajalin muntari?" Yaya yahanasu ta fada tana sakin kuka mai qarfi har da sheshsheqa,tana jin cewa itace da alhakin mutuwar mukhtar,durqushewa tayi sannan ta ja jikinta da qyar ta isa gaban sumayya wadda abdallah ke zaune a kan cinyarta tana dubansh,idanuwanta sun gaji da kuka sai na zuci take wanda yafi ciwo
"Sumayya,don girman Allah,don darajar ma'aiki da iyayenki ki yafemin,babu shakka ina ji a raina nice sikar ajalin muntari,Allah ya bawa muntari mace ta gari,ta daga hankalina na hanaku zaman lpy don kawai baki samu abinda Allah ne kadai ke da ikon bawa bawa ba,na yi masa aure na farko suka rabu bai isheni ishara ba,na sake dauko masa wata na tsaya kai da fata sai da ya kawota cikin rayuwarku,ashe ita ce ajalinsa,itace silar tarwatsa rayuwarku,nayi gaggawa na shiga hurumin ubangiji,idan da na haqura ashe akwai rabon mukhtar bazai taba barin duniya ba sai ya haifi abdullahi,sumayya ki yafemin,kimin afuwa,wallahi na tabbatar idan baki yafemin ba haqqinki bazai taba barina cikin rayuwa ba....." Sai ta kasa qarasa abinda take da niyyar cewa muryarta ta sarqe kamar idanuwanta zash tsiyaye saboda kuka.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now