Babi na sittin da takwas

12.8K 1K 187
                                    

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah yana cewa
*(RANAR QIYAMA YAYIN DA AKA BAWA DAN ADAM LITTAFIN DUKKAN AYYUKANSA ABINDA YA AIKATA SANDA YANA RAYE ZA'A CE DA DAN ADAM)KA KARANTA LITTAFINKA!!!,YA ISHEKA AKAN KANKA KA YIWA KANKA HISABI*

ya subhanallah,ya rahmanu kada kayi mana hisabi ka yafemu.
____________________________________

TEAM ABDUR RAHMAN YA DA SAURIN KARAYA IRIN HAKA NE,NAGA HAR KUN FARA SAREWA FA,ITA FA MACE ALLURAR CIKIN RUWA CE MAI RABO KA DAUKA,KADA 'YAN ADAWA SUYI MUKU DARIYA FA,TAM.
_____________________________________


      Bata sake yunqurin tashi ko motsawa daga wajen ba har zuwa sanda suka iso qasa nijeria,anty dijen na lura da ita,ta kuma kusa ankarewa da dalilin gushewar nutsuwarta,daya daga cikin motocin alfarma dake mallakar mustaphan ita tazo ya kwashe baki daya,kallo daya zaka yi musu ka tabbatar sabuwa ce dal,laila sai bude baki take saboda yadda motar tayi mata dadi,qasa qasa take cewa da sumayya
"Anty sumayya dama kada aje gida don kada mu sauka daga motar nan,dadi wallahi" dariya ta baiwa sumayyan har sautin murmushinta ya fito,hada idanuwa sukayi sanda ya waiwayo yana tsammanin ko wani abun ne ya sake faruwa,da sauri ta kawar da kanta tana gintse dariyar.

          Kowa na ficewa daga motan yayin da yake zaune baiko da niyyar motsawa,amma ta danganta hakan da cewa shi za'a shige da shi cikin gida ne tunda su zasu sauka ne su shiga nasu gidan,tsoron ta yadda zata giftashi ya kamata,duka sun fice saura ita daya,a hankali ta durqusa zuciyarta na bugawa har ta isa bakin qofar inda anty dije ke tsaye tana tsumayin fitowarta din cirar maqullin gidan dake jakar sumayyan,daidai sanda ya fara magana cikin izza da nutsuwa yana baiwa driva umarnin su wuce ciki,kadan ya rage ta fadi anty dije ta tallafeta tana dubanta cikin salon tuhuma
"Wai mene haka sumayya lafiyanki kuwa"
"Bab....babu komai,qafata ce ta harde" bata ce komai ba ta karbi maqullin sannab suka jera zuwa cikin gidan
"Ya kamata ki sanyawa ranki nutsuwa,na fuskanci duk sanda mustapha yayi magana saiki rasa sukuni da nutsuwarki,bafa mukhtar babe,bai kuma san mukhtar ba,kada ki sake ki sake aikata irin gangancin da kika aikata" da sauri ta dubi anty dijen,ya akayi ta karancin halin da take ciki,itama bata sani ba,batasan dalilin da yake sanyawa take kasa controlling kanta ba aduk sanda taji muryarshi wadda ke zubi sak data mukhtar dinta,abinda kawai zai banbanta tashi data dan fi ta mukhtar laushi,bata da bakin magana saboda haka bata ce komai ba jikinta a sanyaye suka qarasa cikin gidan.

       Washe gari haka ta tashi jiki duk a mace,ba dadi haja take ji cikin ranta,bata so anty dije tayi mata wani duba na daban,ba ita ta dorawa kanta ba tasani daga Allah ne,muhimmancin da mukhtar ke da shi a rayuwarta zaiyi wuya tayi saurin mance duk wani abu da yayi kamanceceniya da tashi rayuwar,ba abunda ta iya tsinanawa daga wanka sai kwanciya,ita kanta anty dijen ta lura,sai itama taji ba dadi,tana tsammanin ko fadan data yi mata ne ya sanyata zama haka?.

        Wajen sha biyu ta sameta dakinta tana fitar da kayan da suka dawo da su tana kuma shirya wasu cikin wata jakar daban
"Sumayya,meke damunki?,ko don na miki fada jiya" kamar mai jira sai taji qwalla ta cika mata idanu,kai take girgizawa tana duban anty dijen
"Ba don wani abu yasa na miki magana ba,na fuskanci abinda ke faruwa da ke ne,ina so ki sauya kanki ne" da sauri ta tareta
"Ki daina fadar haka anty,wlh ba haka bane,ke uwa ce a gareni,kina da ikon zartar da duk hukuncin da ya dace da ni,nima bansan me yasa a duk sanda yayi magana nake zamowa haka ba,mukhtar dina nake tunawa anty har yau yaqi barin zuciyata,muryar mukhtar nake ji cikin tasa,sai na dinga jin kamar shine tare da ni" tausayin sumayya ya kamata,ta kama hannuwanta tana duban idanuwanta tana murmushi
"Na fahimceki sumayya,amma shi baisan da haka ba,bana son ya raina min ke ko yayi tunanin wani abu na daban,nafa ji zafin abinda ya miki da fari,ban fadi miki bane saboda yayi ne cikin rashin sani......ki zama jaruma pls,ki dinga tunawa ba shine mukhtar ba....any way,mu ajjiye wannan maganar a gefe,me zakiyi da wadan nan kayan da kike shiryawa a jaka?" Hawayen take gogewa da tafin hannunta itama tana murmushi
"Kano nake so gobe na tafi" idanu ta zaro
"Kano sumayya gobe daga dawowarmu jiya,ko dai wani abun daban aka yi miki?" Marairaice wa tayi
"Don Allah umman khalipha ki daina cewa an min wani abu,kin taba gani uwa ta yiwa 'yarta wani abu ba dai dai ba,kuma diyar ranta ya baci?"
"To idan ba haka ba ai kya bari ko zuwa next week ne atleast ko?,zuwa sannan kin warware gajiyar tafiya kin fidda tsarabar su malam"
"Anty inata kara amma baki gane me nake nufi ba,na qagu any naga abdallah,i missed him alort anty,shima kuma nasan haka ne" kama baki tayi taja dariya
"Iyeeee,lallai yarinya,ga malam ga mama duka su bakiyi missing dinsu ba sai yaronki gaskiya ne" kunya ta kama sumayyan ta kifa kanta saman hannun anty tana dariya qasa qasa,ba zata iya boyewa ba,tabbas tayi missing yaronta
"Shikenan,Allah ya kaimu,amma fa saidai ki bari sai jibi,zamu bude jaka afidda kayan su malam" duk da cewa ba hakan taso ba amma anty dije tafi gaban tayi jayayya da ita haka ta amsa mata da to.

KUNDIN QADDARATAWhere stories live. Discover now